عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ إِذَا رَجَعَ إِلَى أَهْلِهِ أَنْ يَجِدَ فِيهِ ثَلَاثَ خَلِفَاتٍ عِظَامٍ سِمَانٍ؟» قُلْنَا: نَعَمْ. قَالَ: «فَثَلَاثُ آيَاتٍ يَقْرَأُ بِهِنَّ أَحَدُكُمْ فِي صَلَاتِهِ خَيْرٌ لَهُ مِنْ ثَلَاثِ خَلِفَاتٍ عِظَامٍ سِمَانٍ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 802]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Shin dayanku yana son idan ya koma zuwa iyalansa ya samu manyan taguwowi masu ciki masu giba?" muka ce: Eh. Ya ce; "To ayoyi uku dayanku zai karantasu a cikin sallarsa sun fiye masa alheri daga taguwowi uku manya masu ciki".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 802]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa ladan karanta ayoyi uku a cikin sallah; shi ne mafi alheri daga mutum ya sami taguwowi uku masu ciki manya a cikin gidansa.