عن عُقبة بن عامر الجُهني رضي الله عنه قال: قال رسولُ الله صلَّى الله عليه وسلم:
«الجاهِرُ بالقرآن كالجاهِرِ بالصَّدَقَةِ، والمُسِرُّ بالقرآن كالمُسِرِّ بالصَّدَقَة».
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي] - [سنن أبي داود: 1333]
المزيــد ...
Daga Uqubah Dan Amir Al-Juhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Mai bayyanar da Alkur’ani kamar mai bayyanar da sadaka ne, mai boye Alkur’ani kamar mai boye sadaka ne".
[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 1333]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mai bayyanar da karatun Alkur’ani kamar mai bayyanar da bayar da sadaka ne, mai boye karatun Alkur’ani kamar mai boye bayar da sadaka ne.