عن النعمان بن بشير رضي الله عنه قال: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «إن الحلال بيِّن وإن الحرام بين، وبينهما أمور مُشْتَبِهَاتٌ لا يعلمهن كثير من الناس، فمن اتقى الشُّبُهات فقد اسْتَبْرَأ لدينه وعرضه، ومن وقع في الشبهات وقع في الحرام، كالراعي يرعى حول الحِمى يوشك أن يَرْتَع فيه، ألا وإن لكل مَلِك حِمى، ألا وإن حِمى الله محارمه، ألا وإن في الجسد مُضغة إذا صلحت صلح الجسد كله وإذا فسدت فسد الجسد كله ألا وهي القلب».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Nu'aman Dan Bashir -Allah ya yarda da shi- ya ce Naji Manzon Allah yana ewa: "Lallai Halak a bayyane yake, Lallai kuma Haram a bayyane ya ke, kuma a tsakaninsu akawai abubuwa Masu rikitarwa mafi yawan Mutane basu sansu ba, to duk wanda ya gujewa abubuwa masu rikitarwa to hakika ya kubutar da Addininsa da Mutuncinsa, kuma duk wanda ya fada cikin Haram, kamar mai kiwo ne da ya ke kiwo a gefen Gona ya kusa ya fada da Dabbobin sa ciki, ku saurara cewa kowane Sarki yana da Makiyaya, kuma cewa Makiyayar Allah abun da ya haramta, Ku saura ku ji cewa a jikin Mutum akwai wata tsoka idan ta gyaru to jiki ya gyaru baki dayansa kuma idan ta baci to jiki ya baci baki dayansa ku saurara kuji wannan it ce Zuciya".
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi ya bada Misali da duk wanda yake shiga abubuwa masu rikitarwa kamar mai kiwo ne da yake kiwon rakumansa ko Dabbobinsa kusa da wata kasa wacce akwai Makiyaya , kuma Dabbobin Mai kiwon nan sun kusa da su fada cikin ta , kuma ya yi nuni da cewa lallai Ayyuka bayyanannu suna nuna yadda ayyukan boye suke , na ayyukan kirki ko kuma na Barna , kuma yayi bayani cewa Jiki akwai wata tsoka ( ita ce zuciya) jiki yana gyaeuwa idan ta gyaru yana baci idan ta baci.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية
Manufofin Fassarorin