kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

"Lallai halal a bayyane yake kuma haram ma a bayyane yake*, a tsakaninsu akwai wasu al'amura masu rikitarwa da yawa daga mutane ba sa saninsu, wanda ya kiyaye shubuhohi ya kuɓuta a addininsa da mutuncinsa, wanda ya afka cikin shubuhohi ya afka a cikin haram, kamar mai kiwo ne da yake kiwo a gefen shinge ya kusata ya yi kiwo a cikinsa, ku saurara! lallai kowane sarki yana da shinge, ku saurara! lallai shingen Allah shi ne abubuwan da ya haramta, ku saurara lallai! Lallai a jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru jiki ya gyaru dukkaninsa, idan ta ɓaci jiki ya ɓaci dukkaninsa, ku saurara! ita ce zuciya".
عربي Turanci urdu
"Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa*, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, hakuri haskene, Alkur’ani hujjane gareka ko akanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto ta ko ya halakar da ita".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
"Bala'i ba zai gushe ga mumini da mumina ba a kansa da ɗansa da dukiyarsa har sai ya gamu da Allah ba shi da wani laifi".
عربي Turanci urdu
’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amuransa alheri ne, kuma hakan ba ya kasancewa ga kowa sai ga mumini *,idan abin farinciki ne ya same shi sai ya gode wa Allah sai, sai ya zamar masa alheri, idan kuma na sharri ne ya same shi sai ya yi haƙuri, shi ma sai ya zamar masa alheri’’.
عربي Turanci urdu
"Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne ko mai ƙetare hanya"*, Ibnu Umar ya kasance yana cewa: Idan ka kai maraice to kada ka saurari safiya, idan ka wayi gari to kada ka saurari yammaci, ka yi riƙo daga lafiyarka dan rasshin lafiyarka, kuma daga rayuwarka dan mutuwarka.
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya ji tsoronsa ya fi yawa a ciki, kuma duk wanda ya kai matakin kasa, to ya sami matsayi, kawai dai kayan Allah suna da daraja, in ba haka ba kayan Allah ne Aljanna.
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
Cewa wani mutum ya zauna a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah ! ina da bayi biyu suna yi mini karya suna ha'intata suna saba mini, ni kuma ina zaginsu ina dukansu, ya matsayina yake garesu (a urin Allah?) Ya ce: "@Za'a kirga a binda suka ha'inceka suka saba maka suka yi maka karya, da kuma ukubar da ka yi musu*, idan ukubar da ka yi musu gwargwadan laifinsu ne, ya zama daidai wa daida, babu komai gareka ko akanka. Idan ukubar ka akansu kasa da laifin su ne to ya zama falala gareka, idan ukubarka garesu sama da laifin su ne za’a yi masu sakayyar karin daga gareka", ya ce: Sai mutumin yadan yi nesa sai ya fara kuka yana kururuwa, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin ba ka karanta littafin Allah ba: {zamu sanya ma'auni na adalci ga yinin Alkiyama ba za’a zalinci wata rai wani abu ba}. karanta zuwa karshenta, sai mutumin ya ce; Wallahi ya Manzon Allah, ban ji wani abu gareni dasu ba mafi alheri daga rabuwa da su, ina shaida maka cewa su 'ya'ya ne gaba dayansu.
عربي Turanci urdu
Lallai ku wallahi kuna yin wasu Ayyuka mafi siranta daga gashi a Idanuwanku, mu kuma muna xaukar su a lokacin Manzon Allah SAW suna cikin Masu Hallakarwa
عربي Turanci urdu
Idan Allah ya so Alkairi ga bawansa sai ya gaggauta masa Ukuba tun daga Duniya, kuma Idan ya so Sharri da Bawansa sai ya kame ga barin kamashi da laifinsa har sai yaje Ranar Lahira.
عربي Turanci urdu
Annabi SAW ya Zana zanuka, sai ya ce: wannan shi ne Mutum kuma wannan shi ne Ajalinsa yana cikin haka sai zanen mafi kusa yazo masa
عربي Turanci urdu
Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da gani na fuj'a sai ya umarceni in juyar da ido na.
عربي Turanci urdu
"Matsayina da duniya, ni a cikinta ba komai bane sai kamar matafiyi ne akan abin hawa da ya sha inuwa a ƙarƙashin wata bishiya sannan ya tafi ya barta".
عربي Turanci Indonisiyanci
"Kada ku yi hassada, kuma kada ku yi cinikin koɗe (shi ne wani ya zo sayan wani abu sai wani a kasuwar wanda ba ya nufin sayan sai ya zo ya ce a siyar mini a kaza sai ya faɗi sama da kuɗin kayan), kuma kada ku yi gaba, kada ku juyawa juna baya, kuma kada wani ya yi ciniki akan cinikin wani, ku zama bayin Allah 'yan uwan juna* Musulmi ɗan uwan musulmi ne, kada ya zalince shi kuma kada ya ƙi taimakonsa, kada ya wulaƙanta shi tsoron Allah a nan yake" - ya yi nuni zuwa ƙirjin sa, sau uku - "Ya ishi mutum sharri ya wulaƙanta ɗan uwansa musulmi, kowane musulmi akan musulmi haramun ne (ya zubda) jininsa, da dukiyarsa da mutuncinsa". Mutuncinsa".
عربي Turanci urdu
«Ku yi duba zuwa ga wanda yake ƙasa da ku, kada ku yi duba zuwa ga wanda yake sama da ku, hakan zai sa (ku godewa Allah) ba za ku raina ni’imominSa gareku ba».
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
«(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa*: Shugaba adali, da saurayin da ya taso a cikin bautar Allah, da mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallatai, da mutum biyu da suka so juna saboda Allah, sun haɗu saboda Shi kuma suka rabu saboda Shi, da mutumin da mace mai matsayi da kyau ta neme shi sai ya ce: Lallai ni ina jin tsoron Allah, da mutumin da ya yi sadaka sai ya ɓoyeta har (hannunsa) na hagu bai san abinda (hannunsa) na dama ya ciyar ba, da mutumin da ya ambaci Allah shi kaɗai sai idanuwansa suka zubar da hawaye».
عربي Turanci Indonisiyanci