+ -

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: أَخَذَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِمَنْكِبِي، فَقَالَ:
«كُنْ فِي الدُّنْيَا كَأَنَّكَ غَرِيبٌ أَوْ عَابِرُ سَبِيلٍ»، وَكَانَ ابْنُ عُمَرَ، يَقُولُ: إِذَا أَمْسَيْتَ فَلاَ تَنْتَظِرِ الصَّبَاحَ، وَإِذَا أَصْبَحْتَ فَلاَ تَنْتَظِرِ المَسَاءَ، وَخُذْ مِنْ صِحَّتِكَ لِمَرَضِكَ، وَمِنْ حَيَاتِكَ لِمَوْتِكَ.

[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 6416]
المزيــد ...

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne ko mai ƙetare hanya", Ibnu Umar ya kasance yana cewa: Idan ka kai maraice to kada ka saurari safiya, idan ka wayi gari to kada ka saurari yammaci, ka yi riƙo daga lafiyarka dan rasshin lafiyarka, kuma daga rayuwarka dan mutuwarka.

[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6416]

Bayani

Ibnu Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ambata cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe kafaɗarsa - ita ce mahaɗar damuttsa da allan kafaɗa - kuma ya ce masa: Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne, wanda ya zo garin da ba shi da masauki a cikinsa da zai sauka, kuma babu wani mazaunin da zai kwantar masa da rai, ya kaɗaita daga iyalai da 'yan uwa, waɗanda sune sababin shagalta daga Mahalicci, kai ka kasance mafi tsanani daga baƙo shi ne mai ƙetare hanya mai neman ƙasarsa; domin cewa baƙo zai iya zama a garuruwan baƙunta kuma ya zauna a cikinsu, saɓanin mai ketare hanya mai nufin gari, domin cewa daga sha'aninsa saukakawa da rashin tsayuwa, da kwadayi akan saduwa da garinsa, kamar yadda matafiyi ba ya bukatuwa ga sama da abinda zai kai shi zuwa karshen tafiyarsa, haka nan mumini ba ya bukatuwa a duniya sama da abinda zai kai shi wuri.
Sai Ibnu Umar ya yi aiki da wannan nasihar kuma ya kasance yana cewa: Idan ka wayi gari to kada ka jira maraice, idan ka shiga maraice to kada ka jira safiya, ka ƙirga kanka a cikin ma'abota ƙaburbura, kuma cewa rayuwa ba ta kaɗaita daga lafiya da rashin lafiya. Ka yi gaggawa a kwanukan lafiyarka da aikin ɗa'a dan rashin lafiyarka; ka ribaci ayyuka na gari a cikin lafiya kafin rashin lafiya ta tsare tsakaninka da su, ka ribaci rayuwarka a duniya, ka tara abinda zai anfaneka bayan mutuwarka.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الرومانية Malagasy Oromo
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Ɗora tafin malami akan kafaɗar ɗalibi a lokacin koyarwa dan natsarwa da kuma faɗakarwa.
  2. Farawa da nasiha da shiryarwa ga wanda yake neman hakan.
  3. Kyakkyawar koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da buga misalai masu wadatarwa, da faɗinsa: "Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne ko mai ketare hanya".
  4. Saɓanin mutane a tafiyarsu zuwa lahira; mai ƙetare hanya, matsayi ne mafi ɗaukaka a zuhudu daga matsayin baƙo.
  5. Bayanin ƙaranta buri, da yiwa mutuwa tanadi.
  6. Hadisin ba ya nuni akan barin arziƙi da haramta abubuwan jin daɗin duniya; sai dai yana nuni akan kwaɗaitarwa a cikin zuhudu a cikinta, da ƙarantawa daga gareta.
  7. Gaggawa zuwa ga ayyuka na gari kafin lokacin da ba shi da iko akansu, rashin lafiya ko mutuwa su tsare.
  8. Falalar Abdullahi ɗan Umar - Allah - Ya yarda da su - yayin da ya tasirantu da wannan wa'azin daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  9. Ƙasar muminai ita ce aljanna shi baƙo ne a duniya, shi matafiyi ne zuwa gidan lahira, kada ya ratayar da zuciyarsa da wani abu daga baƙunta, kai zuciyarsa mai rataya ce da ƙasarsa wacce zai koma gareta, zamansa a duniya dan ya biya buƙatarsa ne da kuma shirinsa dan komawa zuwa ƙasarsa.