عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«كُلُّ سُلاَمَى مِنَ النَّاسِ عَلَيْهِ صَدَقَةٌ، كُلَّ يَوْمٍ تَطْلُعُ فِيهِ الشَّمْسُ يَعْدِلُ بَيْنَ الِاثْنَيْنِ صَدَقَةٌ، وَيُعِينُ الرَّجُلَ عَلَى دَابَّتِهِ فَيَحْمِلُ عَلَيْهَا أَوْ يَرْفَعُ عَلَيْهَا مَتَاعَهُ صَدَقَةٌ، وَالكَلِمَةُ الطَّيِّبَةُ صَدَقَةٌ، وَكُلُّ خُطْوَةٍ يَخْطُوهَا إِلَى الصَّلاَةِ صَدَقَةٌ، وَيُمِيطُ الأَذَى عَنِ الطَّرِيقِ صَدَقَةٌ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2989]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Kowacce gaɓa daga (jikin) mutane akwai sadaka a kanta, kowanne yinin da rana ta fito a cikin sa da (mutum) zai daidaita tsakanin mutune biyu sadaka ne, kuma ya taimaki mutum game da dabbar sa; sai ya ɗora shi a kanta, ko ya ɗauke masa kayan sa a kanta, to, sadaka ne, kuma kalma mai daɗi sadaka ce, kuma kowanne taku da zai yi zuwa sallah sadaka ne, kuma ya kau da ƙazanta daga hanya sadaka ne".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2989]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa akwai sadaka ta ɗawwu'i saboda Allah - Maɗaukakin sarki - akan kowanne musulmi mukallafi a kowacce rana a kan kowacce gaba daga cikin gabban jikinsa, sadaka ta Nafila ga Allah madaukakin sarki akan tafarkin godiya gare Shi akan lafiya, kuma sanya ƙasusuwansa gaɓɓai zai samu dama da suna damƙa da shinfiɗawa. kuma cewa wannan sadakar tana kaiwa ga ayyukan alheri gabaɗayanta bata tsayuwa akan bada wata dukiya, Daga ciki: Daidaitawarka da yin sulhunka tsakanin masu husuma sadaka ne. A taimakonka ga wani gajiyayye a dabbarsa (abin hawa) sai ka ɗora shi akanta, ko ka ɗauke masa kayansa sadaka ne. Kalma mai daɗi ta zikiri ce da addu'a da sallama da wasunsu sadaka ce. Kowanne takin da ka yi tafiya da shi zuwa sallah sadaka ne, kawar da abinda ake cutuwa da shi a hanya sadaka ne.