+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«صَلَاةُ الرَّجُلِ فِي جَمَاعَةٍ تَزِيدُ عَلَى صَلَاتِهِ فِي بَيْتِهِ وَصَلَاتِهِ فِي سُوقِهِ بِضْعًا وَعِشْرِينَ دَرَجَةً، وَذَلِكَ أَنَّ أَحَدَهُمْ إِذَا تَوَضَّأَ فَأَحْسَنَ الْوُضُوءَ، ثُمَّ أَتَى الْمَسْجِدَ لَا يَنْهَزُهُ إِلَّا الصَّلَاةُ، لَا يُرِيدُ إِلَّا الصَّلَاةَ، فَلَمْ يَخْطُ خَطْوَةً إِلَّا رُفِعَ لَهُ بِهَا دَرَجَةٌ، وَحُطَّ عَنْهُ بِهَا خَطِيئَةٌ، حَتَّى يَدْخُلَ الْمَسْجِدَ، فَإِذَا دَخَلَ الْمَسْجِدَ كَانَ فِي الصَّلَاةِ مَا كَانَتِ الصَّلَاةُ هِيَ تَحْبِسُهُ، وَالْمَلَائِكَةُ يُصَلُّونَ عَلَى أَحَدِكُمْ مَا دَامَ فِي مَجْلِسِهِ الَّذِي صَلَّى فِيهِ، يَقُولُونَ: اللهُمَّ ارْحَمْهُ، اللهُمَّ اغْفِرْ لَهُ، اللهُمَّ تُبْ عَلَيْهِ، مَا لَمْ يُؤْذِ فِيهِ، مَا لَمْ يُحْدِثْ فِيهِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 649]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Sallar mutum a jama'a tana karuwa akan sallarsa agidansa a kasuwarsa da daraja ashirin da wani abu, hakan cewa dayansu idan ya yi alwala ya kyautata alwalar, sannan ya tafi masallaci babu abinda ya zaburo da shi sai sallah, ba ya nufin komai sai sallah, ba zai yi wani taku ba sai an daukaka darajarsa da shi, an kankare masa kuskurensa da shi, har ya shiga masallaci. Idan ya shiga masallaci ya kasance a cikin sallah muddin dai sallah ce ta tsare shi , Mala'iku suna addu'a ga dayanku muddin dai yana mazauninsa wanda ya yi sallah a cikinsa, suna cewa: Ya Allah ka jikansa, ya Allah ka gafarta masa, ya Allah ka karbi tubansa, muddin dai bai cutar ba a cikinsa, muddin dai bai yi (hadasi) kari ba a cikinsa ba".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 649]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa idan musulmi ya yi sallah a cikin jama'a, sallarsa ta kasance tafi sallarsa a gidansa ko kasuwarsa sau ashirin da wani abu. Sannan ya ambaci dalili a hakan: Shi ne cewa mutum idan ya yi alwala sai ya cika alwala ya kyautatata, sannan ya tafi masallaci babu abinda ya fitar da shi sai nufin sallah, ba zai yi wani taku ba sai an daukaka matsayinsa da darajarsa da shi, kuma an shafe masa kuskure da shi, idan ya shiga masallaci ya zauna yana sauraron sallah, to shi yana samun ladan sallah da sakamakonta muddin dai ya jira sallah, Mala'iku suna masa addu'a muddin dai yana mazauninsa wanda ya yi sallah a cikinsa, suna cewa: "Ya Allah Ka gafarta masa, Ya Allah Ka karbi tubansa" muddin dai bai bata alwalarsa ba, ko ya aikata abinda mutane zasu cutu da shi ko Mala'iku ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Sallar mutum daya a gidansa ko kasuwarsa ingantacciya ce, saidai cewa shi yana da zunubi saboda barin jama'a ba tare da wani uzuri ba.
  2. Sallar jama'a a masallaci tafi sallar mutum daya da lada ashirin da biyar ko da shida koda bakwai.
  3. Daga cikin ayyukan Mala'iku addu'a ga muminai.
  4. Falalar tafiya zuwa masallaci mutum yana da alwala.
Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin