عن أبي هريرة رضي الله عنه قال:
أَتَى النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلٌ أَعْمَى، فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، إِنَّهُ لَيْسَ لِي قَائِدٌ يَقُودُنِي إِلَى الْمَسْجِدِ، فَسَأَلَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنْ يُرَخِّصَ لَهُ فَيُصَلِّيَ فِي بَيْتِهِ، فَرَخَّصَ لَهُ، فَلَمَّا وَلَّى دَعَاهُ، فَقَالَ: «هَلْ تَسْمَعُ النِّدَاءَ بِالصَّلَاةِ؟» فَقَالَ: نَعَمْ، قَالَ: «فَأَجِبْ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 653]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Wani mutum makaho ya zo wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ya Ma’aikin Allah! Ba ni da mai jagora da zai ja ni zuwa Masallaci, sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da ya yi masa rangwane da ya yi Sallah a gidansa, sai ya yi masa rangwame, a lokacin da ya juya ya tafi, sai ya kira shi ya ce: shin kana jin kiran Sallah idan aka kira, ya ce: Eh, sai ya ce: Ka amsa.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 653]
Wani mutum makaho ya zo wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ya Ma’aikin Allah ! Ba ni da wanda zai taimaka min ya riƙe hannuna zuwa Masallaci a salloli biyar, yana son Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi masa rangwamen sallar jam’i, sai ya yi masa rangwamen, lokacin da ya juya ya tafi, sai ya kira shi, ya ce; Shin kana jin kiran Sallah? Ya ce; Eh, ya ce: Ka amsawa mai kiran Sallah.