عَن أَبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«تَفْضُلُ صَلاَةُ الجَمِيعِ صَلاَةَ أَحَدِكُمْ وَحْدَهُ، بِخَمْسٍ وَعِشْرِينَ جُزْءًا، وَتَجْتَمِعُ مَلاَئِكَةُ اللَّيْلِ وَمَلاَئِكَةُ النَّهَارِ فِي صَلاَةِ الفَجْرِ» ثُمَّ يَقُولُ أَبُو هُرَيْرَةَ: فَاقْرَءُوا إِنْ شِئْتُمْ: {إِنَّ قُرْآنَ الفَجْرِ كَانَ مَشْهُودًا} [الإسراء: 78].
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 648]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Sallar jam'i ta fi sallar ɗayanku shi kaɗai, da yanki ashirin da biyar, kuma mala'ikun dare da mala'ikun rana suna taruwa a sallar Asuba" Sannan Abu Huraira ya ce: Idan kun so ku karanta: {Lallai karatun alfijir (sallar Asuba) ya kasance abin halartowar (mala'iku) ne} [al-Isra'i: 78].
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 648]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa lada da sakamakon sallar mutum a cikin jama'a tare da liman ya fi sallah ashirin da biyar da mutum zai sallace su shi kaɗai a cikin gidansa ko kasuwarsa, sannan (annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa mala'ikun dare da rana suna taruwa a sallar Asuba, sannan Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce yana mai kafa hujja akan hakan:
Idan kun so ku karanta: {Lallai karatun alfijir (sallar Asuba) ya kasance abin halartar (mala'iku) ne} [al-Isra'a: 78]. Wato: Lallai sallar Asuba mala'ikun dare da mala'ikun rana suna halartarta.