عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ الْأَنْصَارِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا:
أَنَّ رَجُلًا سَأَلَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: أَرَأَيْتَ إِذَا صَلَّيْتُ المَكْتُوبَاتِ، وَصُمْتُ رَمَضَانَ، وَأَحْلَلْتُ الحَلَالَ، وَحَرَّمْتُ الحَرَامَ، وَلَمْ أَزِدْ عَلَى ذَلِكَ شَيْئًا، أَأَدْخُلُ الجَنَّةَ؟ قَالَ: «نَعَمْ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [الأربعون النووية: 22]
المزيــد ...
Daga Abu Abdullahi Jabir ibnu Abdullahi al-Ansari - Allah Ya yarda da su -:
Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Kana ganin idan na sallaci salloli waɗanda aka wajabta, na azimci watan Ramdan, na halatta halal, na haramta haram, ban ƙara komai akan hakan ba, zan shiga Aljanna? Ya ce : «Eh».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [الأربعون النووية - 22]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya sallaci salloli biyar, wadanda suka wajabta bai kara komai akan su ba na nafilifili, kuma ya azimci watan Ramadan bai yi tadawwa’i ba, ya kudirce halatta halal ya kuma aikata shi, ya kudirce haramta haram ya kuma nisanci ta, to shi zai shiga Aljanna.