lis din Hadisai

Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa
عربي Turanci urdu
Wanda ya yi tsayuwar dare a daren Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa
عربي Turanci urdu
An gina musulunci abisa abubuwa biyar
عربي Turanci urdu
Manzon Allah SAW ya Kasance yana E'itikafi a cikin goman kowane Azumin Ramadan, to yayin da shekarar da aka karbi ransa ta zo yayi E'itikafi kwana Ashirin
عربي Turanci urdu
Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi, lallai shi nawa ne kuma nine zan yi sakayya da shi
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ƙoƙari a cikin goman ƙarshe irin ƙoƙarin da ba ya yi a cikin waninsa
عربي Turanci urdu
Lallai cewa wani Mutum ya tambayi Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi game da Azumi a lokacin tafiya sai ya ce: "idan kaga dama kayi Azumi in kuma kaga dama ka sha ruwanka"
عربي Turanci urdu
Cewa Annabi - Tsira da Aminci Allah ya yarda da shi -ya kasance Asuba tana Riske shi a halin yana cikin Janaba daga Ahalinsa, Sannan yayi Wanka yayi Sallah kuma ya yi Azumi"
عربي Turanci urdu
Badaɗayina - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mini wasicci da (abubuwa) uku: Azimin kwana uku a kowane wata, da raka'o'i biyu na walaha, kuma in yi witiri kafin na yi bacci
عربي Turanci urdu
Ya Manzon Allah , Lallai ni nakasan ce nayi Bakance a Jahiliyya cewa Zanyi E'itikafin Dare daya - Kuma a cikin wata Riwaya Kwana daya - a Masallacin Ka'aba? Sai ya ce : to kacika Bakancenka
عربي Turanci urdu
Idan kun ga shi to ku yi azimi, idan kun gan shi ku busha ruwa, idan an ɓoye muku (shi) to ku kaddara (kwanakinsa) sa
عربي Turanci urdu
Duk wanda yake da iko a cikinku to ya yi aure, domin cewa shi ne yafi rintse ido, kuma ya fi katange farji, wanda ba zai iya ba to na umarce shi da azimi, domin shi kariyane gare shi
عربي Turanci urdu
"Ka Sadar da Azumin mu da azumin Ahlulkitab cin Sahur"
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi kyauta cikin mutane, kuma ya kasance mafi kyutar da yake yi a Ramadan ne lokacin da Jibril ya haɗu da shi
عربي Turanci urdu
Cewa Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su Tabbata a gareshi- yayi Azumi Ranar Ashura
عربي Turanci urdu
Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar
عربي Turanci urdu
Bilal yana kiran dare, don haka ku ci ku sha har sai kun ji kiran da Ibn Umm Maktoum ya yi
عربي Turanci urdu
Me ya sa mai yin haila ke rama azumi banda salla? sai ta ce: ke baharuriya ce? sai na ce Ni ba baharuriya bace, kawai dai tambaya nake. sai tace muma muna yin hailar, sai a umarce mu da rama azumi banda salla.
عربي Turanci urdu
“Akwai wata kofa a Sama da ake kira: Rayan, wanda wadanda suke yin azumi za su shiga daga gare ta a Ranar Kiyama, kuma ba wanda zai shiga su sai su, ana cewa: Ina azumin yake? Don haka suka tashi tsaye, ba wanda zai shiga ciki sai su, in sun shiga kuma a rufe yake, ba wanda zai shige shi.
عربي Turanci urdu
Masu buda baki yau sun tafi da Ladan yau
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya yi E'itikafi tare da ni to yayi a goman karshe domin nagani a wannan daren sannan kuma aka ikin ruwa da tabo tun daga , mantar dani, kuma hakika na ganni inayin Sujada a cikin tabo da ruwa safiyarta , to ku nemi riskarta a cikin goman karshe na watan.
عربي Turanci urdu
Na horeku da saukin da Allah ya saukake muku da shi
عربي Turanci urdu
Mun fito tare da Manon Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin watan Azumin Ramalan, cikin wani matsanancin zafin rana, har sai da takai dayanmu yana dora hannunsa akan sa sabida tsananin zafin Rana kuma cikinmu babu mai Azumi sai Manzon Allah in Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi da kuma Abdullahi Dan Rawaha
عربي Turanci urdu
Annabi _ Tsira da Amincin Allah ya yarda da shi - Ya hana Sabi Zarce a Azumi sai suka ce : Cewa ai kaima kana yi sai ya ce: cewa ni ai ba irinku bane , ni ai ana ciyar da ni kuma ana shayar da ni
عربي Turanci urdu
Annabi ya hana yin azumi Ranar jumu'a ne? ya ce: Ey
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya mutu yana da azumi, waliyyinsa zai yi azumi a madadinsa”.
عربي Turanci urdu
Lallai ce wa Mahaifiyata ta Mutu kuma akanta akwai bashin Azumi ko na iya rama mata ? sai ya ce : da ace a kanta akwai bashin kudi zaka biya mata? ya ce: Ey sai ya ce: to Bashin Allah shi yafi cancanta a biya
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Mafi Soyuwar Azumi A wajen Allah shi ne Azumin Annabi Dauda, kuma Mafi soyiwar Sallah Ita ce Sallar Annabi Dauda, ya kasance yana bacci rabin Dare, kuma ya tashi Daya bisa ukun Dare, kuma ya kara Bacci a Daya bisa Shidan Dare, kuma ya kasance yana Azumi yau kuma gobe ya Huta
عربي Turanci urdu
Babu wani azumi sama da azumin dan uwana Dawud - wani bangare na zamani - yayi azumi wata rana bai azumci yini ba
عربي Turanci urdu
"Manzon Allah -tsira da amincin Allah- ya kasance yana kirdadon Azumin Litinin da Alhamis"
عربي Turanci urdu
Manzon Allah ya kasance yana bude baki da danyan dabino kafin yayi salla"
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya yi Azumi daya Saboda Allah Allah zai sanya wani gwalalo tsakaninsa da Wuta kamar nisan Sama da Kasa
عربي Turanci urdu
Idan kayi Azumi Uku a kowane Wata kayi Azumin Sha Uku da Sha Huxu da Sha biyar
عربي Turanci urdu
Lallai Shaidan yana gudu a jikin Mutum kamar yadda jini yake gudu a jikinsa, kuma inajin tsoron kada ya jefa wani sharri a cikin zukatanku ko ya fadi wani abu
عربي Turanci urdu
Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in
عربي Turanci urdu
Mutane ba zasu gushe ba cikin alheri matuƙar sun gaggauta buɗa baki
عربي Turanci urdu
Mun yi sahur tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan ya tashi zuwa sallah, na ce: Nawa ne tsakanin kiran sallah da sahur? ya ce: Gwargwadan ayoyi hamsin
عربي Turanci urdu
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana i'itikafin goman ƙarshe na Ramadan, har Ya koma ga Allah , sannan matansa suka yi i'itikafi a bayansa
عربي Turanci urdu
Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin sahur
عربي Turanci urdu
Kada ku gabaci Ramadan da azimin yini ko yini biyu sai dai mutumin da ya kasance yana yin wani azimi to ya azimce shi
عربي Turanci urdu
Wanda ya manta alhali yana azumi, sai ya ci ko ya sha, to ya cike aziminsa, kaɗai Allah ne Ya ciyar da shi kuma Ya shayar da shi
عربي Turanci urdu
Mun halarci idi tare da Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: "Waɗannan kwanaki biyun Mazon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana azimtarsu: Ranar buɗa bakinku daga aziminku, ɗaya ranar kuma kuna cin abin layyarku a cikinta
عربي Turanci urdu
Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan
عربي Turanci urdu
Ina ganin mafarkenku haƙiƙa sun haɗu a bakwan ƙarshe, duk wanda ya kasance zai yi kardadonsa to ya yi kardadonsa a bakwan ƙarshe
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ta shiga zai raya dare, zai farkar da iyalansa, zai yi ƙoƙari zai ɗaure gwabso
عربي Turanci urdu
Wanda ya azimci zamani (a here) to bai yi azimi ba, azimin kwana uku azimin zamani ne gaba ɗayansa
عربي Turanci urdu
Idan (watan) Ramadan ya zo sai a buɗe ƙofofin aljanna, kuma a kukkule ƙofofin wuta, a ɗaɗɗaure shaiɗanu
عربي Turanci urdu