+ -

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ:
كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَجْوَدَ النَّاسِ، وَكَانَ أَجْوَدُ مَا يَكُونُ فِي رَمَضَانَ حِينَ يَلْقَاهُ جِبْرِيلُ، وَكَانَ يَلْقَاهُ فِي كُلِّ لَيْلَةٍ مِنْ رَمَضَانَ فَيُدَارِسُهُ القُرْآنَ، فَلَرَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَجْوَدُ بِالخَيْرِ مِنَ الرِّيحِ المُرْسَلَةِ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6]
المزيــد ...

Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi kyauta cikin mutane, kuma ya kasance mafi kyutar da yake yi a Ramadan ne lokacin da Jibril ya haɗu da shi, ya kasance yana haɗuwa da shi a cikin kowane dare na Ramadan sai su yi nazaran shi AlƘu'ani, to Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne mafi kyauta ta alheri daga iskar da aka aiko.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi girman mutane a kyauta, ya kasance kyautarsa tana yawaita a cikin watan Ramadan lokacin da ya kasance yana bada abinda yake kamata ga wanda ya kamata, kuma sababi a cikin ƙaruwar kyautarsa abubuwane biyu:
Na farko: Haɗuwarsa da Jibril - aminci ya tabbata agare shi -.
Al'amari na ƙarshe: Karatun AlƘur'ani, shine karatu na zuciya.
Sai nazarin da Jibril - aminci ya tabbata agare shi - yake yi da shi dukkan abinda ya sauka na AlƘur'ani ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne mafi kyauta mafi yawan bayarwa kuma mafi aikata alheri, kuma mafi gaggawar anfanar da halitta daga iska mai daɗi wacce Allah Yake aikota da girgije da kuma rahama.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الدرية الرومانية Malagasy
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin kyautar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da yalwar kayutarsa musamman ma acikin watan Ramadan, cewa shi ne watan ayyukan biyayya da kuma lokutan alkhairai.
  2. Kwaɗaitarwa akan kyauta a cikin kowane lokaci, kuma an so ƙarawa a cikin watan Ramadan.
  3. Yawaita bayarwa da kyauta da kyautatawa da karatun AlƘur'ani a cikin watan Rmadan.
  4. Daga sabubban haddace ilimi akwai karatunsa tare da ɗaliban ilimi da kuma malamai.