عن أنس بن مالك رضي الله عنه قال:
كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَحْسَنَ النَّاسِ خُلُقًا.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2310]
المزيــد ...
Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa kyawawan ɗabi’u.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2310]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa cikar kyawawan ɗabi’u, yana da wannan rigayar a dukkanin kyawawan ɗabi’u, kamar kyakkyawar magana, bayar da kyauta, sakin fuska, rashin cutarwa, juriyarsa ga mutane.