عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«اللهُمَّ إِنَّمَا أَنَا بَشَرٌ، فَأَيُّمَا رَجُلٍ مِنَ المُسْلِمِينَ سَبَبْتُهُ أَوْ لَعَنْتُهُ أَوْ جَلَدْتُهُ فَاجْعَلْهَا لَهُ زَكَاةً وَرَحْمَةً».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2601]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Ya Allah ! Kaɗai ni mutum ne, duk mutum daga cikin musulmai da na zage shi ko na tsine masa ko na dake shi to Ka sanya hakan ya zama tsarki da rahama gare shi».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2601]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya yi addu'a sai ya ce: Ya Allah ? Kaɗai ni mutum ne, ina yin fushi kamar yadda ɗan Adam yake yin fushi, duk muminin da na cutar da shi ko na zage shi na aibanta shi, ko na tsine masa na yi masa mummunar addu'a da korewa daga rahamarKa, ko na dake shi da bulala, to ka sanya hakan ya zama tsarkaka da kusanci da tsarkakewa da kaffara da kuma rahamar da zaka yi masa rahama da ita.