عَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ:
أَنَّ نَبِيَّ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَتَبَ إِلَى كِسْرَى، وَإِلَى قَيْصَرَ، وَإِلَى النَّجَاشِيِّ، وَإِلَى كُلِّ جَبَّارٍ يَدْعُوهُمْ إِلَى اللهِ تَعَالَى، وَلَيْسَ بِالنَّجَاشِيِّ الَّذِي صَلَّى عَلَيْهِ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ.
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1774]
المزيــد ...
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rubuta (wasiku) zuwa ga Kisra, da Ƙaisara, da Najjashi, kai da dukkan mai tsaurin kai, yana kiransu zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, amma ba Najjashin da Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sallah ba.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1774]
Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kafin rasuwarsa ya yi rubutu zuwa ga waɗanda ke kewaye da shi daga sarakunan al'ummu, yana kiransu zuwa ga Musulunci; sai ya rubuta zuwa ga Kisra, shi laƙabi ne na dukkanin wanda yake sarki ne na Farisawa, haka zuwa ga Ƙaisara shi kuma laƙabi ne na dukkanin wanda yake sarki ne na Rum, haka zuwa ga Najjashi shi laƙabi ne na dukkanin wanda yake sarki ne na Habasha. Kuma ya rubuta zuwa ga kowane sarki mai tsaurin kai wanda ya yi wa mutane tumbe, ya rinjaye su, kuma Anas - Allah Ya yarda da shi - ya bayyana cewa Najjashin da aka rubuta masa ba Najjashin da ya musulunta ba ne kuma ya rasu Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa sallah.