+ -

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ:
لَمَّا نَزَلَتْ: {إِنَّا فَتَحْنَا لَكَ فَتْحًا مُبِينًا لِيَغْفِرَ لَكَ اللهُ} إِلَى قَوْلِهِ {فَوْزًا عَظِيمًا} [الفتح: ١-٥] مَرْجِعَهُ مِنَ الْحُدَيْبِيَةِ، وَهُمْ يُخَالِطُهُمُ الْحُزْنُ وَالْكَآبَةُ، وَقَدْ نَحَرَ الْهَدْيَ بِالْحُدَيْبِيَةِ، فَقَالَ: «لَقَدْ أُنْزِلَتْ عَلَيَّ آيَةٌ هِيَ أَحَبُّ إِلَيَّ مِنَ الدُّنْيَا جَمِيعًا».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1786]
المزيــد ...

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Lokacin da waɗannan ayoyin suka sauka: {Lallai Mu mun yi maka buɗi buɗi mabayyani dan Allah Ya gafarta maka} har zuwa faɗinSa: {Rabo mai girma} [al-Fath: 1-5] lokacin dawowarsa daga Hudaibiyya, alhali su baƙin ciki da ɓacin rai yana cakuɗe da su, alhali haƙiƙa annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya soke hadayarsa a Hudaibiyya, sai ya ce: "Haƙiƙa an saukar mini da wata aya ita ce mafi soyuwa gareni daga duniya da abinda ke cikinta baki ɗaya".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1786]

Bayani

Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa lokacin da faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki - ya sauka ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: {Haƙiƙa mu mun yi maka buɗi buɗi mabayyani (1). Dan Allah Ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubinka da wanda ya jinkirta, kuma Ya cika ni'imarSa gareka kuma Ya shiryar da kai hanya madaidaiciya (2). Kuma Ya taimake ka taimako mai girma (3). Shi ne wanda Ya sanya nutsuwa a cikin zukatan muminai dan su ƙara imani tare da imaninsu, rundunonin sammai da ƙasa nasa ce, kuma Allah Ya kasance Masani Mai hikima (4). Dan ya shigar da muminai maza da mata aljannatai ƙoramu suna gudana ta ƙarƙashinsu suna masu dawwama a cikinsu kuma Ya kankare musu munananan ayyukansu hakan ya kasance rabo mai girma a wurin Allah} [al-Fath: 1-5]. A lokacin dawowarsa daga Hudaibiyya, su kuma sahabbai bakin ciki da bacin rai ya turnuke su, kuma an hana su yin Umarah, saboda abinda sulhun ya faru a kansa da kuma zatansu cewa sulhun ba’a yi shi akan maslahar musulmai ba, hakika kuma sun yanka hadaya a Hudaibiyya, sai (annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Haƙiƙa an saukar mini da wata aya wacce ita ce mafi soyuwa gareni daga duniya bakiɗayanta sannan ya karantata.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin girman abinda Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya yi ni'ima da shi ga annabinSa Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - na buɗi mai girma a cikin sulhun Hudaibiyya; inda Ya ce masa: {Lallai ne mu mun yi maka buɗi buɗi mabayyani} ayoyi biyu.
  2. Bayanin abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi baiwa da shi ga sahabbai - Allah Ya yarda da su - lokacin da suka bi umarninsa kuma suka jawu, inda aka saukar musu da faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -: {Dan ya shigar da muminai maza da muminai mata aljannatai waɗanda ƙoramu suke gudana daga ƙarƙashinsu}. karanta ayar har ƙarshe.
  3. Bayanin falalar Allah ga annabinSa, da kuma muminai cewa ya yi musu alƙawarin buɗi da kuma nasara.
  4. Al-Sa'adi ya faɗa a cikin Tafsirinsa akan wannan ayar: {lallai ne Mu Mun yi maka buɗi buɗi mabayyani}.
  5. [al-Fath: 1], wannan buɗin da aka ambata shi ne sulhun Hudaibiyya, lokacin da mushirikai suka hana manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - lokacin da ya zo yana mai yin Umarah a cikin ƙissa mai tsawo, wacce ƙarshen al'amarinta ya zama cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi sulhu akan jingine yaƙi tsakaninsa da su shekara goma, kuma akan ya yi Umarah a shekara ta gaba, kuma akan cewa wanda ya yi nufin ya shiga cikin alƙawarin Kuraishawa da taimakonsu to zai shiga, wanda kuma ya so ya shiga cikin alƙawarin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - to zai yi, saboda haka ne lokacin da mutane suka samu aminci sashinsu ga sashi, sai fadin Da'awah zuwa ga addinin Allah ta yalwatu, kuma kowane mumini ya zama a kowane guri a cikin wadancan yankunan, zai iya samun hakan, mai kwadayin tsayuwa akan hakikanin musulunci zai iya yi wuwa ya yi, sai mutane a cikin wannan lokacin suka shiga cikin addinin Allah jama'a jama'a, saboda haka ne Allah ya ambace shi budi, kuma Ya siffanta shi da cewa budi ne bayyananne, wato: Zahiri mabayyani, hakan domin cewa manufa a cikin bude garuruwan mushrikai shi ne daukaka addinin Allah, da kuma taimakon musulmai wannan kuwa ya faru da wannan buɗin.
Fassara: Turanci Indonisiyanci Sinhalese Vietnam Swahili Asami الهولندية الغوجاراتية الرومانية المجرية الجورجية
Manufofin Fassarorin