عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ:
كُنَّا فِي غَزَاةٍ فَكَسَعَ رَجُلٌ مِنَ المُهَاجِرِينَ رَجُلًا مِنَ الأَنْصَارِ، فَقَالَ الأَنْصَارِيُّ: يَا لَلْأَنْصَارِ، وَقَالَ المُهَاجِرِيُّ: يَا لَلْمُهَاجِرِينَ، فَسَمَّعَهَا اللَّهُ رَسُولَهُ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَا هَذَا؟» فَقَالُوا: كَسَعَ رَجُلٌ مِنَ المُهَاجِرِينَ رَجُلًا مِنَ الأَنْصَارِ، فَقَالَ الأَنْصَارِيُّ: يَا لَلْأَنْصَارِ، وَقَالَ المُهَاجِرِيُّ: يَا لَلْمُهَاجِرِينَ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «دَعُوهَا فَإِنَّهَا مُنْتِنَةٌ» قَالَ جَابِرٌ: وَكَانَتِ الأَنْصَارُ حِينَ قَدِمَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَكْثَرَ، ثُمَّ كَثُرَ المُهَاجِرُونَ بَعْدُ، فَقَالَ عَبْدُ اللَّهِ بْنُ أُبَيٍّ: أَوَقَدْ فَعَلُوا، وَاللَّهِ لَئِنْ رَجَعْنَا إِلَى المَدِينَةِ لَيُخْرِجَنَّ الأَعَزُّ مِنْهَا الأَذَلَّ، فَقَالَ عُمَرُ بْنُ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: دَعْنِي يَا رَسُولَ اللَّهِ أَضْرِبُ عُنُقَ هَذَا المُنَافِقِ، قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «دَعْهُ، لاَ يَتَحَدَّثُ النَّاسُ أَنَّ مُحَمَّدًا يَقْتُلُ أَصْحَابَهُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 4907]
المزيــد ...
Daga Jabir Ibnu Abdullah -Allah Ya yarda da su - ya ce:
Mun kasance a cikin wani yaƙi, sai wani mutum daga cikin Muhajirun ya daki bayan wani mutum daga cikin mutanen Madina, sai mutumin Madina ya ce: Yaku mutanen Madina ku kawo mini agaji, wanda ya yi hijira kuma ya ce: Yaku muhajirai ku kawo mini agaji, sai Allah Ya jiyar da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: «Mene ne wannan?» sai suka ce: Wani mutum ne daga Muhajirun ya daki bayan wani mutum daga cikin mutanen Madina, sai mutumin Madinan ya ce: Yaku mutanen Madina ku kawo mini agaji, wanda ya yi hijira kuma ya ce: Yaku Muhajirun kukawo mini agaji, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ku barta lallai ita (ɗabi'a ce) mai wari ». Jabir ya ce: Mutanen Madina sun kasance a lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo Madina sun fi yawa, sannan Muhajirun suka yi yawa bayan nan, sai Abdullahi Ibnu Ubay ya ce: Shin sun aikata kuwa, wallahi idan muka koma Madina sai maɗaukaka sun fitar da maƙasƙanta, sai Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya Manzon Allah ka barni in daki wuyan wannan munafikin, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «ka bar shi, kada mutane suce lallai (Annabi) yana kashe sahabbansa».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 4907]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana halin tafiya a wani yaƙi a tare da shi akwai sahabbansa Muhajirun da kuma Ansarawa - Allah Ya yarda da su -, sai wani mutum daga Muhajirun ya daki bayan wani mutum daga Muhajirun da hannunsa. Sai mutumin Madinan ya ce: Ku taimakeni yaku Ansarawa, wanda kuma ya yi hijira ya ce: Ku taimakeni yaku Muhajirun, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ji sai ya ce: Mene ne wannan? Sai suka ce: Wani mutum ne daga Muhajirai ya daki bayan wani mutum cikin Ansarawa da hannunsa, sai mutumin Madinan ya ce: Ku kawo mini agaji yaku Ansar, wanda ya yi hijira kuma ya ce: Ku kawo min agaji yaku Muhajirun. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ku bar wannan al'adar ta Jahiliyya domin ita mummuna ce abar ƙyama mai cutarwa; ita ce cewa mutum idan abokin rigimarsa ya rinjaye shi sai ya kira mutanensa sai su yi gaggawar taimakonsa alhali shi ne ya kasance azzalimin ko kuma shi ne wanda aka zalinta dan jahilci dake garesu da kuma ƙabilanci. Jabir ya ce: Ansarawa sun kasance lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo Madina yana mai hijira sune mafi yawa, sannan bayan nan Muhajirun suka yi yawa. Sai shugaban munafukai Abdullahi Ibnu Ubayy ibnu Salul ya ce: Al'amarin yakai wannan haddin?! Wallahi idan muka koma Madina sai masu rinjaye - wato yana nufin shi da waɗanda ke tare da shi - sun fitar da ƙasƙantattu - wato yana nufin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da waɗanda ke tare da shi daga Madina. Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya Manzon Allah ƙyaleni in daki wuyan wannan munafukin, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: ƙyale shi, dan kada mutane su dinga cewa Muhammad yana kashe mabiyansa ko da azahiri ne.