عن أبي بكرة رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم:
«أَلَا أُنَبِّئُكُمْ بِأَكْبَرِ الْكَبَائِرِ؟» ثَلَاثًا، قَالُوا: بَلَى يَا رَسُولَ اللهِ، قَالَ: «الْإِشْرَاكُ بِاللهِ، وَعُقُوقُ الْوَالِدَيْنِ» وَجَلَسَ وَكَانَ مُتَّكِئًا، فَقَالَ: «أَلَا وَقَوْلُ الزُّورِ»، قَالَ: فَمَا زَالَ يُكَرِّرُهَا حَتَّى قُلْنَا: لَيْتَهُ سَكَتَ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2654]
المزيــد ...
Daga Abu bakrata - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?" sau uku, suka ce: na'am ya Manzon Allah, ya ce: "Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye" sai ya zauna alhali ya kasance a kishingiɗe, sai ya ce: "Ku saurara da faɗar zur" ya ce: Bai gushe ba yana maimaitata har sai da muka ce: Ina ma dai ya yi shiru.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2654]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba wa sahabbansa labari game da mafi girman zunubai, sai ya ambaci waɗannan ukun:
1. Yi wa Allah shirka: Shi ne juyar da kowanne nau'in ibada ga wanin Allah, da daidaita wanin Allah da Allah a AllantakarSa da UbangidantakarSa da sunayenSa da siffofinSa.
2. Saɓawa iyaye: Shi ne kowacce irin cutarwa ga iyayen, magana ce ko aiki, da barin kyautatawa musu.
3. Faɗin zur, shaidar zur tana daga ciki: Shi ne dukkanin maganar da take ƙarya ce da aka yi nufin tauye wanda ta faɗa kansa ta hanyar ƙwace dukiyarsa da keta mutuncinsa, ko makamancin hakan.
Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya maimaita gargaɗi game da faɗin zur don faɗakarwa a kan muninta da mummunan gurbinta ga zamntakewa, har sai da sahabbansa suka ce: Ina ma dai ya yi shiru don tausaya masa, da kuma ƙin abin da zai tayar masa da hankali.