Karkasawa: Fiqihu da Usulunsa . Jinaya . Diyya .

عن أبي هُرَيْرة رضي الله عنه قال: «اقْتَتَلَتْ امْرَأَتَانِ مِنْ هُذَيْلٍ، فرمَت إحداهما الأخرى بحجر، فَقَتَلَتْهَا وَمَا فِي بَطْنِهَا فَاخْتَصَمُوا إلَى النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم فَقَضَى رسول الله: أَنَّ دِيَةَ جَنِينِهَا غُرَّةٌ- عَبْدٌ، أَوْ وَلِيدَةٌ- وَقَضَى بِدِيَةِ المرأة على عَاقِلَتِهَا، وَوَرَّثَهَا وَلَدَهَا وَمَنْ مَعَهُمْ، فَقَامَ حَمَلُ بنُ النَّابِغَةِ الهُذَلِيُّ، فَقَالَ: يا رسول الله، كيف أغرم من لا شَرِبَ وَلا أَكَلَ، وَلا نَطَقَ وَلا اسْتَهَلَّ، فَمِثْلُ ذَلِكَ يُطَلُّ؟ فقال رَسول الله صلى الله عليه وسلم : «إنما هذا من إخوان الكُهَّان» من أجْل سَجْعِهِ الَّذِي سَجَعَ.
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

An karbo daga Abi Huraira-Allah ya yarda dashi-yace"Mata biyu daga Huzail sun yi fada.Sai daya daga cikinsu ta jefi daya da Dutse,sai ta kasheta da abinda yake cikinta sai sukayi Husuma zuwa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi sai Manzan Allah yayi musu Hukunci:cewa Diyyar Dan cikinta ya zamo Gurra-wato Bawa,ko Baiwa-sai yayi Hukunci da Diyyar Matar akan Makusantanta,kuma Danta zai gajeta da wanda suke tare dasu,sai Dan Alnabiga Alhuzali ya tashi,yace:Ya Rasulallah,ya zan biya wanda bai sha ba bai ci ba,kuma bai Magana ba baiyi Kuka ba,kamar misalin wannan ake bari?sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace:"Hakika wannan yana daga yan Uwan Bokaye"saboda saja'in da ya tsara.
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Mata biyu sun yi Husuma daga Kabilar Huzail,sai Daya daga cikinsu ta jefi Daya da Dutse Karami,wanda galibi baya kisa,saidai cewa shi ya kasheta ya kuma kashe Tayinta da yake cikinta.Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi Hukunci da cewa Diyyar Dan Tayin,Bawa ko Baiwa,dai-dai ne Dan tayin Namiji ne ko Mace,kuma Diyyarsa tana kan wacce tayi kisan.Kuma yayi Hukunci ga Matar da aka kashe da Diyya,domin kisan nata kisa ne mai kama da ganganci,kuma yana kan Yan-uwar Matar,domin an gina tane abisa Taimakekeniya da Adalci,kuma saboda kisan bana ganganci bane.Kuma domin cewa Diyya gado ce ta wacce aka kashe saboda haka Danta da wadanda suke tare dashi a Magada sune zasu karbeta,sauran Yan-uwa basu da komai daga gareshi.Sai Hamalu Dan Al-Nabiga-shine Mahaifin wacce tayi kisan- yace:Ya Ma'aikin Allah,yaya zamu biya wanda akai barinsa amace,bai taba ci ba ,bai taba sha ba,bai taba magana ba,har agane rayuwarsa da hakan?ya fadi hakan da Usulubin Zance abin yiwa saja'i.Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya kyamaci Maganar tasa,saboda abin dake cikinta na raddin hukunce-hukuncen shari'a da irin wannan saja'oin dorawa kai masu kama da saja'oin Bokaye wadanda suke cin Dukiyoyin Mutane da ita bada .Gaskiyaba

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Portuguese Malayalam
Manufofin Fassarorin
kashe kashe