عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنْ تَرَدَّى مِنْ جَبَلٍ فَقَتَلَ نَفْسَهُ فَهُوَ فِي نَارِ جَهَنَّمَ يَتَرَدَّى فِيهِ خَالِدًا مُخَلَّدًا فِيهَا أَبَدًا، وَمَنْ تَحَسَّى سُمًّا فَقَتَلَ نَفْسَهُ فَسُمُّهُ فِي يَدِهِ يَتَحَسَّاهُ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدًا مُخَلَّدًا فِيهَا أَبَدًا، وَمَنْ قَتَلَ نَفْسَهُ بِحَدِيدَةٍ فَحَدِيدَتُهُ فِي يَدِهِ يَجَأُ بِهَا فِي بَطْنِهِ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدًا مُخَلَّدًا فِيهَا أَبَدًا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5778]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Wanda ya gangaro daga wani dutse sai ya kashe kansa to shi yana cikin wuta zai dinga gangarowa a cikinta yana abin dawwamarwa a cikinta har abada, wanda ya tsotsi wata gubar sai ya kashe kansa to gubarsa tana hannunsa zai dinga tsotsarta a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada, wanda ya kashe kansa da wani ƙarfe to ƙarfen zai zama a hannunsa zai dinga cakawa cikinsa shi a cikin wutar Jahannama yana madawwami har abada a cikinta».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5778]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya yi gangancin kashe kansa gargaɗi a duniya cewa za’a yi masa uƙuba a ranar alƙiyama a cikin wutar Jahannama ta irin hanyar da ya yi wa kansa a duniya dan sakamakon da ya dace, wanda ya faɗo daga saman dutse sai ya kashe kansa to shi yana cikin wutar Jahannama zai dinga faɗowa a cikinta daga dutsen Jahannama zuwa kwarinta yana madawwami a cikinta, wanda ya kwankwɗi wata guba sai ya kashe kansa da ita to gubarsa tana hannunsa zai dinga kwankwaɗarta a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada, wanda ya cakawa kansa wani karfe a cikinsa sai ya kashe kansa, to karfensa yana hannunsa zai dinga sukar kansa da shi a cikinsa a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada.