عن عبد الله بن عمرو بن العاص رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«الْكَبَائِرُ: الْإِشْرَاكُ بِاللهِ، وَعُقُوقُ الْوَالِدَيْنِ، وَقَتْلُ النَّفْسِ، وَالْيَمِينُ الْغَمُوسُ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 6675]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Amr Dan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Manyan zanubai su ne: Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye, da kashe rai, rantsuwa mai dulmiyarwa".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6675]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana manyan zunubai cewa su ne waɗanda aka yi narko (alƙawarin azaba) a kan wanda ya aikata su da narko mai tsanani a duniya ko a lahira.
Na farkonsu "Yi wa Allah shirka": Shi ne karkatar da kowanne nau'i daga Nau’ukan ibada ga wanin Allah, da daidaita wanin Allah da Allah cikin abin da ya keɓanci Allah a AllantakarSa da UbangidantakarSa da sunayenSa da siffofinSa.
Na biyunsu: "Saɓawa iyaye": Shi ne dukkanin abin da yake nuna cutarwa ga iyaye; magana ce ko aiki, da barin kyautata musu.
Na ukunsu "Kashe rai": ba tare da wani haƙƙi ba, kamar kisa a kan zalunci da ta'addanci.
Na huɗunsu "Rantsuwa mai dulmiyarwa": Ita ce rantsuwa alhali yana mai ƙarya yana sane cewa ƙarya yake, an ambaceta da hakan; domin cewa tana dulmiya mai yinta a laifi sannan a wuta.