kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

"Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?*" sau uku, suka ce: na'am ya Manzon Allah, ya ce: "Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye" sai ya zauna alhali ya kasance a kishingiɗe, sai ya ce: "Ku saurara da faɗar zur" ya ce: Bai gushe ba yana maimaitata har sai da muka ce: Ina ma dai ya yi shiru.
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa*)) suka ce: Ya Manzon Allah, wadanne ne su? Ya ce: “Shirka da Allah, da sihiri, da kashe rai wacce Allah Ya haramta sai da gaskiya, da cin riba, da cin dukiyar maraya, da juya baya ranar yaki, da yiwa mumina katangaggiya rafkananniya kazafi".
عربي Turanci urdu
"Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda ya kashe da wanda aka kashe suna cikin wuta*", sai na ce: Ya Manzon Allah, wannan mai kisan ne, to, mene ne laifin wanda aka kashe? ya ce: "Lallai shi ma ya kasance mai kwaɗayi ne a kan kashe ɗan uwansa".
عربي Turanci urdu
"Kaɗai kwatankwacin abokin zama na gari da mummunan abokin zama, kamar maɗaukin almiskine da mai busa zugazugi,* maɗaukin alimiski: Kodai ya baka, ko kuma ka saya daga gare shi, ko kuma ka samu ƙanshi mai daɗi daga gare shi, mai busa zugazugi kuwa: Kodai ya ƙona kayanka, ko kuma ka samu mummunan ƙanshi daga gare shi".
عربي Turanci urdu
"Ba'a wani rai da zalunci sai idan ya kasance Xan Annabi Adam na farko yana da Alhaki a cikin sadomin shi ne wanda ya Sunnata kisa"
عربي Turanci urdu
"Duk al'ummata an yafe musu sai masu bayyanarwa*, kuma yana daga bayyanarwa mutum ya aikata wani aiki (mummuna) da daddare, sannan ya wayi gari Allah Ya rufa masa asiri, sai ya ce: Ya (ya falalarsa kansa) wane, jiya da daddare na aikata kaza da kaza, alhali ya kwana Uabangijinsa Ya rufa masa asiri, shi kuma ya wayi gari yana tona asirin da Allah Ya rufa masa".
عربي Turanci urdu
An tambayi Annabi game da abu mafi yawa da yake shigar da Mutane" Al-janna? ya ce: Tsoron Allah da kyawawan Halaye, kuma aka tambaye shi game da abu mafi yawa da yake jefa Mutane wuta sai ya ce Baki da Farjin su"
عربي Turanci urdu
Bana baku labari ba Maye cizo? shi ne Gulmar da ake yada kadarta cikin Mutane
عربي Turanci urdu
Qararrawa ita ce garayar Shaixan ce
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
Wani mutum ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: @Ya Manzon Allah, shin kana ganin idan wani mutum ya zo yana son karɓar kuɗina?* Ya ce: «‌Kada ka ba shi kuɗinka)) Ya ce: Shin kana ganin idan ya yaƙe ni? Ya ce: «‌Ka yaƙe shi» Ya ce: Shin kana ganin idan ya kashe ni? Ya ce: «‌Kai shahidi ne». Ya ce: Shin kana ganin idan na kashe shi ? Ya ce: «‌Shi yana cikin wuta»
عربي Turanci urdu
«Lokacin da aka hau da ni (aka yi Mi'iraji da ni) na wuce wasu mutane da suke da farata na tagulla, suna yakusar fuskokinsu da ƙirazansu da su*, sai na ce: Su waye waɗannan ya Jibril, ya ce: Waɗanan sune waɗanda suke cin naman mutane, kuma suke afkawa cikin mutuncinsu».
عربي Turanci urdu
«‌Mutum uku Allah ba zai yi musu magana ba a ranar alƙiyama kuma ba zai tsarkakesu ba kuma suna da zaba mai raɗaɗi*: Dattijo mazinaci, da talaka mai girman kai, da mutumin da ya sanya Allah wata haja, ba ya sayarwa kuma ba ya siya sai da rantsuwarsa».
عربي Turanci urdu
"Idan Allah ya so yiwa wasu Mutane Azaba, sai Azabar ta sami wadanda suke cikin su, Sannan sai a tashe su a kan Ayyukansu"
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
«Wanda ya gangaro daga wani dutse sai ya kashe kansa to shi yana cikin wuta zai dinga gangarowa a cikinta yana abin dawwamarwa a cikinta har abada*, wanda ya tsotsi wata gubar sai ya kashe kansa to gubarsa tana hannunsa zai dinga tsotsarta a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada, wanda ya kashe kansa da wani ƙarfe to ƙarfen zai zama a hannunsa zai dinga cakawa cikinsa shi a cikin wutar Jahannama yana madawwami har abada a cikinta».
عربي Turanci Indonisiyanci
«Na haneku da ƙananan zunibai*, kaɗai misalin ƙananan zunubai kamar mutane ne da suka sauka a cikin wani kwari, sai wannan ya zo da ice, wannan ma ya zo da ice, har suka sa gurasarsu ta nuna, kuma lallai ƙananan zunubai a duk lokacin da aka kama mai aikatasu saboda su zasu halaka shi».
عربي Turanci Indonisiyanci