جُنْدُبُ بن عبد اللهِ البجلي رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ -صلى الله عليه وسلم -: «كان فيمن كان قبلكم رجل به جُرْحٌ فَجَزِعَ؛ فأخذ سكِّينا فحَزَّ بها يده، فما رَقَأَ الدم حتى مات، قال الله عز وجل : عبدي بَادَرَنِي بنفسه، حرمت عليه الجنة».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Jundubu Dan Abdullahi Albujali -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "An yi wani mutum cikin wadanda suka gabace ku yana da wani ciwo sai ya yanke kauna, ya dauki wuka ya yanke hannunsa, jini bai dauke ba har ya mutu. Sai Allah yace: Bawa na ya rigaye ni da kansa, don haka Na haramta masa Aljanna".
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah ya bawa sahabbansa labarin wani utum cikin al'ummar da suka gabace mu ya kasance yana da wani rauni mai azabar ciwo, sai ya karaya ya yanke kauna da warkewa, ya kasa yin hakuri da azabar da yake sha, ko dan neman lada ma a wajen Allah, saboda karancin imani da sakankancewa da Allah, sai ya dauki wuka ya yanke hannnun da ita, sai jini ya yi ta zuba, yaki tsayawa har mutumin ya mutu. Sai Allah yace: Maanar abin da yace: Wannan bawa na ne ya kagara ga zuwan rahama ta da waraka ta, ba shi da dauriya kan jarabawa ta, saiya yi gaggawar hallaka kansa, yayi tsammanin ya rage ajalinsa ta hanyar kashe kansa, sai Na haramta masa shiga Aljanna,, wanda aka haramtawa Aljanna kuwa, to wuta ce makomarsa.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam
Manufofin Fassarorin