+ -

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ حَلَفَ عَلَى يَمِينٍ وَهُوَ فِيهَا فَاجِرٌ لِيَقْتَطِعَ بِهَا مَالَ امْرِئٍ مُسْلِمٍ، لَقِيَ اللَّهَ وَهُوَ عَلَيْهِ غَضْبَانُ». قَالَ: فَقَالَ الْأَشْعَثُ: فِيَّ وَاللَّهِ كَانَ ذَلِكَ؛ كَانَ بَيْنِي وَبَيْنَ رَجُلٍ مِنَ الْيَهُودِ أَرْضٌ، فَجَحَدَنِي، فَقَدَّمْتُهُ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ لِي رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَلَكَ بَيِّنَةٌ؟» قُلْتُ: لَا. قَالَ: فَقَالَ لِلْيَهُودِيِّ: «احْلِفْ». قَالَ: قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِذَنْ يَحْلِفَ وَيَذْهَبَ بِمَالِي. فَأَنْزَلَ اللَّهُ تَعَالَى: {إِنَّ الَّذِينَ يَشْتَرُونَ بِعَهْدِ اللَّهِ وَأَيْمَانِهِمْ ثَمَنًا قَلِيلًا}. إِلَى آخِرِ الْآيَةِ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2416]
المزيــد ...

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Duk wanda ya rantse akan wata rantsuwa alhali shi yana fajiri a cikinta dan ya ci dukiyar wani mutum musulmi, to zai gamu da Allah alhali Shi yana Mai fushi akansa". ya ce: Sai Ash'As ya ce: Wallahi a kaina hakan ya kasance; ya kasance akwai wani fili tsakanina da wani mutum cikin Yahudawa, sai ya yi min musun filin, sai na kawo shi ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce dani: "Shin kana da shaidu?" Na ce: A'a. Ya ce: Sai ya cewa Bayaahudan: "Ka rantse". Ya ce: Na ce: Ya manzon Allah, to sai ya rantse ya tafi da dukiyata. Sai Allah - Maɗaukin sarki - ya ce: {Lallai ne wadanda suke musanya alkawarin Allah da rantse-rantsensu da wani farashi dan kadan}. har zuwa ƙarshen ayar,

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2416]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga yin rantsuwa tare da sanin mai rantsuwar cewa shi maƙaryaci ne a cikinta, dan ya ya karbi dukiyar waninsa; to zai gamu da Allah alhali Yana mai fushi da shi. Sai Ash'As ɗan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa , Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi hakan lokacin da ya kasance akwai rigima ta mallakar wani fili tsakaninsa da wani mutum cikin Yahudawa, sai suka kai ƙara zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya cewa Ash'As: Wajibi ne ka zo da shaidun da suke tabbatar da abinda kake ƙararsa, idan ka kasa to baka da wani abu sai rantsuwar abokin rigimarka wanda ake ƙararsa, sai al-Ash'As ya ce: Ya manzon Allah, to bayahude zai rantse kuma ba ya taka tsantsan ya tafi da dukiya ta, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da gasgata hakan a cikin Alƙur'ani a faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -: {Lallai waɗanda suke musanya}. Suke canja {da alƙawarin Allah}, da wasiyyarSa ga muminai da dawo da amana {da rantse-rantsensu} da rantsuwarsu da sunanSa suna maƙaryata {ɗan kudi kaɗan} na rabon duniya {To waɗannan basu da wani rabo a lahira} kuma basu da wani nasibi {Kuma Allah ba Zai yi musu magana ba}, da zancen da zai faranta musu rai ya amfanar da su ba, kai ya yi fushi da su, {Kuma ba Zai kallesu ba a ranar alƙiyama} kallo na rahama da kyautatawa, {Kuma ba Zai tsarkakesu ba} da yabo mai kyau ba, kuma ba Zai tsarkakesu da gafara daga zunubai da datti ba {Kuma azaba mai raɗaɗi ta tabbata a garesu} mai sa ciwo saboda abinda suka aikata.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hani daga halatta dukiyoyin mutane da ƙarya.
  2. Kaurara haƙƙoƙin musulmai a ƙanƙanin haƙƙi da mai yawansa.
  3. Shaidu suna kan mai kawo ƙara, rantsuwa kuma tana kan wanda aka kai ƙara idan ya musa.
  4. Tabbatar da haƙƙi da shaidu biyu, idan ba’a samu shaidu a wurin mai ƙara ba, to rantsuwa ta wajaba akan wanda aka kai ƙara.
  5. Haramta rantsuwa (mai dulmiyarwa) ita ce ta ƙarya wacce mai rantsuwa yake ƙwace haƙƙin waninsa da ita, kuma ita tana daga cikin manyan zunubai, wacce take bijirar da mai ita ga fushin Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma uƙubarSa.
  6. Shugaba ya yi wa abokanan rigima wa'azi, musamman ma a lokacin nufin yin rantsuwa.
Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Asami الهولندية الغوجاراتية الرومانية المجرية الجورجية
Manufofin Fassarorin