+ -

عن عبد الله بن عباس رضي الله عنهما أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «لو يُعْطَى الناسُ بدَعْوَاهُم لادَّعى رجالٌ أموالَ قومٍ ودِمَاءَهُم، لكنَّ البينةَ على المدَّعِي واليَمِينَ على من أَنْكَرَ».
[صحيح] - [أخرجه بهذا اللفظ البيهقي في السنن الكبرى. وأخرج البخاري ومسلم بعضه]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Abbas - Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Da ace ana bawa Mutane abu sabida ikirarin cewa nasu ne da da yawa daga cikin Mutane sunyi Da'awar Dukiyoyin wasu Mutane da jininsu, sai dai wanda duk yai Da'awa to shi zai kawo Dalili Rantsuwa kuwa tana kan wanda ya Musanta."
Ingantacce ne - Al-Baihaki ne Ya Rawaito shi

Bayani

Hadisin Tushe ne cikin bayanin abunda yasa baza'a karbi Da'awa haka zikau ba ba tare da wasu Dalilai ba ko Alamomi, da kuma rantsar da wanda yai musu; don tabbatar da Adalci, da tsayar da Gaskiya, da kuma kare Rayuka da Dukiya, to duk wanda yai Da'awar wani abu ba tare da dalili ba to Da'awarsa abar Mayar masa ce kuma duk Daya ne ta kasance a ikin Hakkoki ne da kuma sauran Ma'amaloli ko kuma a cikin Wasu Mas'aloli na Imani da kuma Ilimi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin