lis din Hadisai

Jibril bai gushe ba yana yi min wasiyya da maƙoci, har sai da na yi zaton cewa shi zai sa shi ya yi gado
عربي Turanci urdu
ya yi hani daga bakance, ya ce: "Lallai shi ba ya zuwa da alheri, kawai ana fitar da shi ne daga marowaci
عربي Turanci urdu
Lallai ni wallahi - in Allah Ya so - bana rantsuwa, sai inga waninta mafi alheri daga gareta. sai na yi kaffarar rantsuwata, kuma nazowa wanda shi ne mafi alherin
عربي Turanci urdu
Wanda yake son Allah Ya tseratar da shi daga baƙin cikin ranar Alƙiyama, to, ya yaye wa wanda yake cikin wani mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (wani haƙƙi ko nauyin da ya ke kansa)
عربي Turanci urdu
Ya Manzon Allah, ina da makwabta biyu, to a ba ni wa? Ya ce: «Zuwa ga mafi kusantar su da kai».
عربي Turanci urdu
Babu sauran Hijira bayan ancigarin Makka da yaki sai dai akwai Jahadi da Niyya, kuma idan aka nemi ku futo yaki to futo
عربي Turanci urdu
"Duk waanda yayi zalunci dani daya na kasa, za'a ciccibo masa tun daga Kasan Bakwai"
عربي Turanci urdu
"Lallai cewa Manzon Allah ya hana Al-Munabaza: Kuma yana nufin Mutum ya jefa Rigarsa zuwa wani Mutum kafin ya juyashi, ko ya dubashi, kuma ya hana Al-Mulamasa: kuma yana nufin Mutum ya taba Tufa ba zai kalle ta ba"
عربي Turanci urdu
"Lallai Manzon Allah ya hana saida "yayan Itatuwa har sai sun bura, aka ce Maye Bura din yace har sai ya fara yin ja, ya ce baka ganin idan Allah ya hana 'yayan Itattun suyi, to da me mutum zai rama kudin Dan Uwansa?
عربي Turanci urdu
Cewa - Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya hana sai da yayan itace har sai sun bura ya hana mai saye da kuma mai sayarwa
عربي Turanci urdu
Azirfa da zinare riba ne, sai hannu da hannu, alkama da alkama riba ne, sai hannu da hannu, sha'ir da sha'ir riba ne, sai hannu da hannu, dabino da dabino riba ne, sai hannu da hannu
عربي Turanci urdu
Annabi ya hana Dan Gari ya siyarwa da Dan Kauye, (kayansa a Kasuwa), kuma kada kuyi keta, kuma kada wani daga cikinku yayi ciniki akan cinikin Dan Uwansa, kuma kada ya nemi Aure kan neman Auren Dan Uwansa
عربي Turanci urdu
Cewa Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su Tabbata a gareshi- "Annabi ya hana saida Zinare da Azurfa Bashi
عربي Turanci urdu
"Manzon Allah ya hana Sayar da Azurfa da Azurfa, da Zinare da Zinare, Sai dai dai da dai dai, Kuma ya Umarce mu Mu sayar da Azurfa da Zinare, duk yadda muka so, kuma mu sayi Zinare da Azurfa yadda Muka so"
عربي Turanci urdu
Babu wani ma'abocin zinare ko azirfa, da ba ya bada haƙƙinsu daga garesu, sai a ranar alƙiyama ya kasance za'a ƙerasu a siffar alluna na wuta
عربي Turanci urdu
Wanda ya rantse ya ce: Ni barrantacce ne daga Musulunci, kuma idan maƙaryaci ne, to ya kasance kamar yadda ya faɗa, kuma idan ya kasance mai gaskiya, to ba zai dawo Musulunci ba cikin kwanciyar hankali
عربي Turanci urdu
Idan mutum ya rasu akin sa ya yanke sai dai daga abu uku: Sadaka mai gudana, ko wani ilimin da ake anfanuwa da shi, ko ɗa na gari da ya ke masa addu'a
عربي Turanci Indonisiyanci
Ya Manzon Allah, lallai Ummu Sa'ad ta rasu, to wace sadaka ce tafi?. Ya ce: "Ruwa". Ya ce: Sai ya haƙa wata rijiya, ya ce: Wannan ga Ummu Sa'ad ce
عربي Turanci Indonisiyanci
Sa'ad Dan Ubada ya yi wa MAanzon Allah fatawa game da alwashi da mahaifiyarsa ta yi, wanda hara ta murtu bata cika shi ba? , sai Manzon Allah tsira da amincin Allah yace: sai ka yi mata
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya rantse kan wata rantsuwada ya takure kansa da ita yana son karvar Dukiyar wani Musulmi, kuma a halin Qarya ya ke, zai gamu da Allah SWT yana fushi da shi
عربي Turanci urdu
Yar uawata tayi bakancen zata je dakin Allah babu Takalmi, sai ta \umarce ni da na tambayi Manzon Allah SAW sai na tambaye shi, sai ya ce: ta tafi kuma tana iya hawan abin hawa
عربي Turanci urdu
Ya kai Abdurrahman Dan Samra, Kada ka nemi Mulki, sabida Idan aka baka sabida kai ka nema to sai abarka da ita
عربي Turanci urdu
Wanda ya yi rantsuwa sannan ya ga cewa Allah yana jin tsoron ta, to sai taqawa ta zo
عربي Turanci urdu
Wani mutum da ya gabace ku an yi ma hisabi, kuma babu wani abin alheri a gare shi, sai dai kawai ya gauraya da mutane kuma yana cikin walwala, kuma ya kasance yana umartar yaransa maza biyu su wuce wahala. Kwace shi
عربي Turanci urdu
Domin idan dayanku ya dauki mace mai ciki, to dutsen ya zo, sai ya kawo wani dunkulen itace a bayansa ya sayar, to Allah ya rufe fuskarsa da shi, ya fi masa fiye da ya tambayi mutane, su ba shi ko su hana shi
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya turke Doki Saboda Allah, don yayi Imani da Allah, kuma ya gasgata da Alkawarinsa, to cewa koshinsa da kuma Ruwansa da Bayan gidansa da futsarinsa ya na cikin abunda za'a auna Masa lada a Ranar Al-kiyama
عربي Turanci urdu
Annabi -SAW- ya sayi rakumi daga wurinsa, kuma ya auna masa shi kuma ya auna.
عربي Turanci urdu
Idan kun dafa kayan yaji, sai ku kara ruwa, kuma ku yi wa makwabta alkawari
عربي Turanci urdu
"Lallai Kabilar Ash'ariyawa idan Mujinsu ya Mutu a wajen yaki, ko Abincin Iyalansu ya ragu a Madina"
عربي Turanci urdu
"Na yi Kyautar Jakin dawa ga Manzon Allah -tsra da Amincin Allah su tabbata a gare shi"
عربي Turanci urdu
;Bai da ce ga Musulmi ba yana da wani abun hannu da zai iya yin wasiyya da shi; ya zauna kwana biyu face sai ya rubuta ta kasance a rubce tare da shi
عربي Turanci urdu
"Duk wanda ya ga ainahin kudinsa a wajen wani da ya tsiyace -ko wani Mutum- to shi ne mafi cancanta da shi ba wani ba"
عربي Turanci urdu
Cewa Annabi -Tsira da Amincin allah su tabbata a gareshi - ya sayi abinci daga Bayahude kuma ya jinginar masa da Silkensa na Karfe
عربي Turanci urdu
Ya Rasulallah, Lallai nidai na samu wata kasa a khaibar, kuma ban sami wani kudi ko daya ita ce mafi tsadar abin da na mallaka, mai kake umarta ta da ita?sai ya ce: idan kaso kayi sanya asalinta Hubusi, ko kuma kayi Sadaka da ita
عربي Turanci urdu
Wayyo, Wayyo, Wannan tsantantsar ribace, kada kayi, kuam sai dai idan kanason ka saya to ka siyar da dabinonka da wani cinikin daban, sannan ka saya da kudin
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su tabbata a garesu- "cewa lallai Annabi ya hana cin kudin kare, Da Sadakin karuwanci, da kuma ladan boka".
عربي Turanci urdu
ko kana ganin na yi ta yi maka tayi don in kwace maka Rakuminka? Karbi Rakuminka da kudinka, na barmaka shi
عربي Turanci urdu
Kar ka saye shi, kar ka dawo da sadakar da ka yi, ko da kuwa dirhami daya aka sayar maka, don kuwa mai karbar abin da ya yi kyauta da shi: kamar mai komar da aman da ya yi ne
عربي Turanci urdu
Mai fasa kyautarsa, kamar mai dawowa ne cikin Amansa
عربي Turanci urdu
Duk wanda zai yi rancen wani abu to yai rance cikin Sanannen Ma'auni, da kuma Mizani Sananne, kuma zuwa lokaci Sananne
عربي Turanci urdu
"Mun Kasance Mafi yawan Mutanen Madina kuma mun kasance muna bada hayar Fili, kan cewa wannan namu ne, Kuma wannan na, wani lokaci wata gonar tayi wata kuma atki futar da komai sai ya hana mu wannan, Amma da Azurfa: bai hana mu ba"
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya Yanta wani Rai Musulmi to Allah zai Yanta da kowace Gaba daga jikinsa daga Wuta, har Al-aurarsa da Al-aurarsa
عربي Turanci urdu
Kun yi rantsuwa mai yawa a cikin siyarwa, saboda ciyarwa, to, sai ta fita
عربي Turanci urdu
Ga ɗayanku ya koma ga rantsuwarsa a cikin danginsa, ya yi zunubi tare da Allah - Maɗaukaki - ya ba da kaffarar da Allah ya ɗora masa.
عربي Turanci urdu
Sulaiman Xan Dauda -Amincin Allah a gare shi ya ce: "Na rantse a wannan Daren zan taki Matana guda Saba'in kowace mace daga cikin su zata haifi Yaron da zaiyi jahadi a Tafarkin Allah
عربي Turanci urdu
Ka riqe wani vangaren na dukiyarka yafi maka Al-kairi
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya 'yanda rabonsa na Bawan da sukai tarayya a cikinsa kuma yana da kuxin da zai iya cika ragowar kuxin sai a lissafa masa sauran rabon sauran ya biya don bawan ya 'yantu
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya 'yanta rabonsa na wani bawa to ya wajaba akansa ya cika sauran a cikin kuxinsa, idan bashi da shi sai ayi kimar bawan yayi aikin fansa
عربي Turanci urdu
Mutane Uku suna da Lada biyu: wani Mutum daga cikin Ahlul-Kitab da yayi Imani da Annabinsa, kuma yayi Imani da Annabi Muhammad, da kuma Bawan da ya bada Hakkin Allah da Hakkin Mai gidansa, da Kuma Mutumin da ya ke da baiwa ya kyautata tarbiyantar da ita, kuma ya sanar da ita kuma ya kyautata Sanar da ita, sannan ya Yantata sannan kuma ya Aureta, to yana da lada biyu.
عربي Turanci urdu
"Lallai wata Mata ta zo Wajen Manzon -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- da Wata Riga da aka saka"
عربي Turanci urdu
"lallai Annabi ya Hana siyar da Walittaka ko kyautarta"
عربي Turanci urdu
Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yazo min don ya dubani shekarar Hajjin ban-kwana daga wani ciwo da yayi tsanani agareni,sai nace:Ya Ma'aikin Allah,hakika ciwo yakai inda yakai agareni kamar yadda kake gani,kuma ni Ma'abocin Dukiya ne,bamai gadona sai 'ya mace bana yi Sadaka da Biyu bisa Ukun Dukiyata ba?yace:a'a,nace:Rabi fa ya Ma'aikin Allah?yace:a'a,nace:Daya bisa Ukufa?yace:Daya bisa Uku,kuma Daya bisa Uku da yawa,hakika cewa kai kabar Magadanka Mawadata shi yafi akan kabarsu Talakawa suna rokon Mutane,kuma cewa kai ba zaka ciyar da wata ciyarwa ba kana mai neman Fuskar Allah face Allah ya baka lada da ita,hatta abinda zaka saka a Bakin Matarka.Yace:Nace ya Ma'aikin Allah zan barwa abokanaina a bayana?yace:Hakika cewa kai ba za'a barka ba ka aikata wani aiki da kake neman Fuskar Allah sai ka kara Daraja dashi da Daukaka,kuma watakila kuma idan aka barka har wasu su amfana da kai wasu kuma su cutu da kai,ya Allah ka cikawa Abokanaina Hijirarsu,kada ka juyar dasu a bayansu,sai dai sadauki shine Sa'ad Dan Khaula(yana yiwa Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-Rasa'i don ya Rasu a Makka)
عربي Turanci urdu
Ka ku tari hanya, kuma kada dayanku yayi cikin akan cinikin Dan uwansa, kuma kada kuyi keta, kuma kada Mutumin birni ya siyarwa da Mutumin kauye kayansa, kuma kada ku daure hantsar rakuma ko dabbobi
عربي Turanci urdu
Cewa Annabi -Allah ya yarda da shi- yayi wa Yan khaibar Mu'amala da rabin abunda yake futowa daga garin na Dabino ko Shuka
عربي Turanci urdu
"Cewa Manzon Allah yayi sauki cikin cinikin Al-araya, cikin Buhu biyar ko kasa da buhu biyar"
عربي Turanci urdu
"Lallai cewa Annabi yayi rangwame ga mai Ariyya: ya siyar da ita kafin ta bushe"
عربي Turanci urdu
An tambayi Annabi game da tsintuwar zinare da azurfa? sai ya ce: Ka sanar dabuhunta da kuma madaurinsa, sannan kayi shela shekara, idan ba'a samu mai ita ba sai ka yi sadaka da ita, kuma ta amanto ajiya ce a wurinka to idan Mai ita yazo wata rana; sai ka biyashi
عربي Turanci urdu
Babu wani Sauran Maraici bayan Balaga, ko kuma hakurin wuni zuwa dare
عربي Turanci urdu
Sayyadin Abubakar -Allah ya yarda da shi- ya shiga wajen wata Mata daga Kabilar Ahmas ana kiranta da Zainab, sai ya ganta bata Magana
عربي Turanci urdu
"Bawa da aka Mallaka Mai gyara yana da Lada Biyu"
عربي Turanci urdu
Cewa shi ya ambaci wani Mutum daga cikin Bani isra'ila, ya tambayi wasu daga cikin Bani Isra'ila cewa ya ranta masa Dinari dubu, sai ya ce: kazo mun da shaidu da zan kafa shaida da su, sai ya ce: Allah ya bisa Shaida, yace: to kazo mun da mai lamini, yace: Allah ya isheni lamini, ya ce: Kayi gaskiya, sai ya bashi kudin zuwa wani lokaci
عربي Turanci urdu
Allah ya bawa dukkan Mai Haqqi Haqqinsa, kuma babu wata Wasiyya ga mai Gado, Kuma Xa na Ubansa ne, Kuma Karuwa za'a jefeta ne, Kuma duk wanda ya danganta Kansa zuwa Wanin Mahaifinsa ko Maulansa don yana qyamarsu to la'antar Allah ta tabbata a gare shi, Kuma Allah ba zai karvi wani aiki ko sadaka daga gare shi ba
عربي Turanci urdu
Kun ganni na bakwai a cikin Bakwai Bakwai. Ba mu da wani bawa sai wanda ya mari karaminmu, don haka Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umurce mu da 'yantar da ita
عربي Turanci urdu
Maye ya xagaka ya kai Baban Huzaim?
عربي Turanci Fassara Yaren Faransanci
Annabi Isa xan Maryam yaga wani Mutum yana sata, sai ya ce da shi: Kayi sata? saiya ce: aa na rantse da Allah wada babu wani Ubangiji sai shi, sai Isa ya ce nayi Imani da Allah,kuma idona ya nunan Qarya
عربي Turanci Fassara Yaren Faransanci
Wanda ya yanki haƙƙin wani mutum musulmi da rantsuwarsa, to haƙiƙa Allah Ya wajabta wuta gare shi, kuma Ya haramta masa aljanna" sai wani mutum ya ce: Koda wani abune ɗan kaɗan ya Manzon Allah? ya ce: "Koda kara ne na itaciyar ƙirya
عربي Turanci urdu
Wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba mumini ba ne», aka ce: Waye ya Manzon Allah? ya ce: «Wanda maƙocinsa ba ya aminta daga sharrinsa
عربي Indonisiyanci Sinhalese
Zinare da zinare, azirfa da azirfa, alkama da alkama, sha'ir da sha'ir, dabino da dabino. gishiri da gishri, (dole su zama) tamka da tamka, daidai da daidai (a lokacin da za’a yi canji), idan waɗannan jinsinan suka canza, to ku siyar yadda kuke so idan ya zama hannu da hunnu ne
عربي Turanci Indonisiyanci