عن زيد بن خالد الجهني رضي الله عنه : «سئل رسول الله صلى الله عليه وسلم عن لُقَطَة الذهب، أو الوَرِق؟ فقال: اعرف وكِاَءَهَا وعِفَاصَهَا، ثم عَرِّفْهَا سَنَةً، فإن لم تُعرَف فاستنفقها، ولتكن وديعة عندك فإن جاء طالبها يوما من الدهر؛ فأدها إليه. وسأله عن ضالة الإبل؟ فقال: ما لك ولها؟ دَعْهَا فإن معها حِذَاَءَهَا وسِقَاءَهَا، تَرِدُ الماء وتأكل الشجر، حتى يجدها رَبُّهَا. وسأله عن الشاة؟ فقال: خذها؛ فإنما هي لك، أو لأخيك، أو للذئب».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Zaid Dan Khalid Aljuhani -Allah ya yarda da shi- "An tambayi Annabi game da tsintuwar zinare da azurfa? sai ya ce: Ka sanar dabuhunta da kuma madaurinsa, sannan kayi shela shekara, idan ba'a samu mai ita ba sai ka yi sadaka da ita, kuma ta amanto ajiya ce a wurinka to idan Mai ita yazo wata rana; sai ka biyashi" kuma an tambaye shi game da tsintuwar Rakumi sai ya ce: "Mai ya hada da ita? ka barta sabida tana da takalminta da ruwanta, tana iya shan ruwa kuma taci bishiya har mai ita ya sami abarsa, kuma aka tambaye shi game da tsintuwar Akuya sai ya ce: "ka dauketa; domin kodai ta zama rabonka ko na Dan uwanka ko kuma na kura"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Wani Mutum ya tambayi Annabi game da hukuncin Dukiyar da ta bata daga Mai ita ta zinare da Azurfa da kuma Rakuma da Dabbobi, sai Annabi ya bayyana Hukunci wadan nan abubuwa don su zamanto misali ga sauran abubuwan da suka yi kama da su, na Dukiyoyin da suka bata, sai su Dauki Hukuncinsu, sai ya ce game da Zinare da Azurfa: Ka yi bayanin abinda aka daure ta shi da kuma gidan da aka saka ta a cikinsa, don mai ita ya iya gane ta, sai kuma ka Jarraba duk wanda ya ce tasa ce don ka gane gaskiyarsa, to idan abin da ya fada ya dace da abinda yake hakika sai ka bashi abarsa, in ba haka kuma ba bai dace da hakikanin yadda take ba, to zai ci gaba da cigiya har tsawon shekara daga tsintuwar, kuma zai rika yi a wurin taron mutane, kamar Kasuwanni, da kofofin Masallatai, da wuraren taruwar Jama'a, da kuma inda ya tsinceta, sannan an halatta masa bayan cigiyarsa tsawon shekara, ba'a samu mai ita ba to yayi Sadaka da ita amma idan mai ita ya zo a kowane lokaci komai tsawonsa to ya bashi abarsa, amma batanccen Rakumi da Mai kama da shi wanda zai iya kare kansa, to an hana tsintuwarsa, domin baya bukatar kariya, a Dabi'arta tana da kariyar kanta, don tana da karfin kare kanta daga kana nan Dabbobi, kuma tana takonta da zata iya zuwa ko ina, da wuyanta da zaya iya yin kiwo daga bishiya da kuma ruwa, kuma tana da tankin da zata iya ajiye abinci a cikinta, kuma tana iya kare kanta har mai ita ya same tawanda yake ta nemanta daga inda ta bata, kuma amma batattun akuyoyi da masu kama da su na daga kananan Dabbobi, to an umarci a tsince su kada su Hallaka ko kuma kuraye su cinye su, kuma bayan tsintar u mai u zai zo ya karbi abinsa, ko kuma su zauna tsawon shekara ana cigiya sai ta zama ta wanda take hannunsa.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Portuguese
Manufofin Fassarorin