+ -

عن عبد الله بن عباس رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم يوم فتح مكة: «لا هجرة بعد الفتح، ولكن جهاد ونية. وإذا اسْتُنْفِرْتُم فَانْفِرُوا. وقال يوم فتح مكة: «إن هذا البَلد حَرَّمَهُ الله يوم خلق الله السموات والأرض، فهو حَرَامٌ بحُرْمَةِ الله إلَى يوم القيامة، وإنه لم يحل القتال فيه لِأَحَدٍ قَبْلِي، ولم يَحِلَّ لي إلا ساعة من نهار، حرام بِحرمة الله إلى يوم القيامة، لا يُعْضَدُ شَوْكُهُ، وَلاَ يُنَفَّرُ صَيْدُهُ، وَلاَ يَلْتَقِطُ لُقَطَتَهُ إلا من عَرَّفَهَا، ولاَ يُخْتَلَى خَلاَهُ». فقال العباس: يا رسول الله، إلا الإِذْخِرَ؛ فإنه لِقَيْنِهِمْ وبيوتهم؟ فقال: «إلا الإِذْخِرَ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Abbas Allah ya yyarda da shi ya ce: Manzon Allah ya ce Ranar bude Makka: "Babu sauran Hijira bayan ancigarin Makka da yaki sai dai akwai Jahadi da Niyya, kuma idan aka nemi ku futo yaki to futo, kuma ya ce: Ranar bude Lallai cewa wannan garin Allah ya haramta shi tun ranar da ya halicci sama da kasa, kuma yana nan da haramcin yana nan har zuwa ranar Alkiyama, kuma cewa ba'a taba halattawa wani ba shi kafin ni, kuma ba'a halatta mun ba nima sai dan wani lokaci ne na dan rana, kuma haramce da haramtawar Allah har zuwa ranar Alkiyama, ba'a tunbuke kayarta, kuma ba'a korar farautar ta kuma ba'a tsintar tsintuwar ta sai ga wanda zai shelantata, kuma ba'a yankar ciyawarta, sai Abbas ya ce ya Manzon Allah sai dai Jemarsa ko; domin dashi mutane suke rufin dakinsu da dangarsu? sai ya ce Sai Jemarsa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Abdullahi Dan Abbas yana bada labarin cewa Annabi ya tsaya yana mai Huduba ranar bude Makka, sai ya ce Babu wata sauran Hijira yana nufin daga Makka; don ta ama garin Musulunci, sai dai kawai Jihadi yana nan kuma yayi Umarnin duk wanda ake nemi ya fito zuwa Jihadi to ya futo don nuna biyayya ga Allah da Manzonsa da kuma Jagora, sannan yai bayanin Haramcin Makka, kuma ya ambaci cewa wannan haramcin tun lokacin da aka halicci sammai da kasa ya kekuma ba'a taba halastawa wani ita ba kafin Annabi, kuma ba zata taba halatta ga kowa ba kuma bayansa kuma shima an halasta masa ita ne wani Dan lokaci na rana sannan kuma Haramcin ya kuma dawowa, sannan kuma ya sake fadin haramcin Makka kan cewa ba'a sare kayar ta kuma ba'a korar Farautar ta kuma ba'a tsintar tsintuwar ta sai ga wanda zai shelanta ta kuma ba'a yankar ciyawarta sai dai an iyakance jemarta sabida bukatar Mutanen Makka.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin