عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيَّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ -وَكَانَ غَزَا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ثِنْتَيْ عَشْرَةَ غَزْوَةً- قَالَ: سَمِعْتُ أَرْبَعًا مِنَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَعْجَبْنَنِي، قَالَ:
«لاَ تُسَافِرِ المَرْأَةُ مَسِيرَةَ يَوْمَيْنِ إِلَّا وَمَعَهَا زَوْجُهَا أَوْ ذُو مَحْرَمٍ، وَلاَ صَوْمَ فِي يَوْمَيْنِ: الفِطْرِ وَالأَضْحَى، وَلاَ صَلاَةَ بَعْدَ الصُّبْحِ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ، وَلاَ بَعْدَ العَصْرِ حَتَّى تَغْرُبَ، وَلاَ تُشَدُّ الرِّحَالُ إِلَّا إِلَى ثَلاَثَةِ مَسَاجِدَ: مَسْجِدِ الحَرَامِ، وَمَسْجِدِ الأَقْصَى، وَمَسْجِدِي هَذَا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1995]
المزيــد ...
Daga Abu sa'id AlKhudr - Allah Ya yarda da shi - ya kasance ya yi yaƙi tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yaƙi goma sha biyu - ya ce: Na ji abubuwa hudu daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai suka ƙayatar dani, ya ce:
"Kada mace ta yi tafiya, tafiyar kwana biyu sai da mijinta tare da ita ko muharraminta, Babu azumi a ranaku biyu: Karamar sallah da babbar sallah, kuma babu sallah bayan asuba har sai rana ta bullo, kuma babu bayan la'asar har sai ta fadi, kuma ba'a daure sirdi (nikar gari domin tafiya) sai a masallatai uku: Masallaci mai alfarma, da masallacin Kudus, da masallacina wannan".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1995]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana abubuwa hudu:
Na farkonsu: Hana mace daga tafiyar kwana biyu ba tare da mijinta ba ko daya daga muharramanta ba, shi ne wanda ta haramta agare shi haramci na har'bada daga 'yan uwa, kamar Da, da uba, da Dan dan uwa da dan 'yar uwa, da baffa da kawu, da makamancin hakan.
Na biyunsu: Hani daga azimin ranar ƙaramar sallah da ranar babbar sallah, duk daya ne musulmi ya azimce su ne akan bakance (alwashi) ko nafila, ko kuma kaffara.
Na ukunsu: Hani daga sallar nafila bayan sallar la'asar har sai rana ta fadi, da bayan bullowar alfijir har sai rana ta bullo.
Na hudunsu: Hani daga tafiya zuwa wani wuri daga wurare da ƙudirce falalarsu da ƙudirce ninkin kyawawan lada a cikinsu, in banda wadannan masallatan uku, to ba'a daure sirdi ga wasunsu dan yin sallah a cikinsu, domin lada ba'a ninkashi sai a wadannan masallatan uku: Masallaci mai alfarma (Dake Makka), da masallacin Annabi (Dake Madina), da masallacin Kudus (Dake Falasdin).