عَنْ عُقْبَةَ بْنَ عَامِرٍ الْجُهَنِيَّ رضي الله عنه قَالَ:
ثَلَاثُ سَاعَاتٍ كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَنْهَانَا أَنْ نُصَلِّيَ فِيهِنَّ، أَوْ أَنْ نَقْبُرَ فِيهِنَّ مَوْتَانَا: حِينَ تَطْلُعُ الشَّمْسُ بَازِغَةً حَتَّى تَرْتَفِعَ، وَحِينَ يَقُومُ قَائِمُ الظَّهِيرَةِ حَتَّى تَمِيلَ الشَّمْسُ، وَحِينَ تَضَيَّفُ الشَّمْسُ لِلْغُرُوبِ حَتَّى تَغْرُبَ.
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 831]
المزيــد ...
Daga Uƙuba ɗan Amir al-Juhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Lokuta uku Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana hana mu yin salla a cikinsu, ko binne mamatanmu a cikinsu:
Lokacin da rana ta fito a bayyane har sai ta ɗaga, da kuma lokacin da ta tsaya a tsakiyar sama har sai ranar ta karkace, da kuma lokacin da ranar ta kusa faɗuwa har sai ta faɗi.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 831]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani a yi sallar nafila a lokuta uku, ko a yi ƙabari a binne matattu a cikinsu: Lokaci na farko: Lokacin da rana zata fito a bayyane, hakan a yayin farkon ɓullowarta har sai ta ɗaga gwargwadan goron mashi, shi ana ƙaddara shi da kwatankwacin rubu'in sa'a (minti sha biyar). Na biyu: Lokacin da rana ta tsaya a tsakiyar sama, to babu inuwa gareta ta ɓangaren gabas ko yamma har sai ta karkace daga tsakiyar sama, inuwa ta bayyana daga ɓangaren gabas yayin da farkon lokacin sallar Azahar yake farawa, kuma taƙaitaccen lokaci ne; shi gwargwadan kwatankwacin minti biyar ne. Na uku: Loakcin da ta karkace rana ta fara faɗuwa har sai ta faɗi.