عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«الدُّنْيَا مَتَاعٌ، وَخَيْرُ مَتَاعِ الدُّنْيَا الْمَرْأَةُ الصَّالِحَةُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1467]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
Duniya jin daɗi ce, fiyayyen jin daɗin duniya shi ne mace ta gari.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1467]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin cewa ita duniya da abin da ke cikinta wani abu ne da za a ji dadi da shi, na wani lokaci sannan ya wuce, to, mafificin jin daɗinta shi ne mace ta gari, wacce idan ya kallaceta za ta faranta masa, idan kuma ya umarceta za ta yi masa biyayya, idan ba ya nan za ta tsare shi a kanta da kuma dukiyarsa.