عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمنينَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا زَوْجِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَعْتَكِفُ العَشْرَ الأَوَاخِرَ مِنْ رَمَضَانَ، حَتَّى تَوَفَّاهُ اللَّهُ، ثُمَّ اعْتَكَفَ أَزْوَاجُهُ مِنْ بَعْدِهِ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2026]
المزيــد ...

Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -:
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana i'itikafin goman ƙarshe na Ramadan, har Ya koma ga Allah , sannan matansa suka yi i'itikafi a bayansa.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi] - [Sahih Al-Bukhari - 2026]

Bayani

Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya lazimci i'itikafi a goman ƙarshe na Ramadan, dan neman Lailatul Qadr, kuma ya zarce akan hakan har zuwa lokacin da Allah Ya ɗauki ransa, haƙiƙa matansa - Allah Ya yarda da su - sun lazimci i'itikafi a bayansa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Halaccin i'itikafi a cikin masallatai, har ga mata akan wasu iyakoki na shari'a, da kuma sharaɗin aminta daga fitina.
  2. I'itikafi yana ƙarfafa a cikin goman ƙarshe na Ramadan saboda lazimtar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  3. I'itikafi Sunna ne mai zarcewa ba'a shafe shi ba, dan matansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun yi i'itikafi a bayansa.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (44)