عن أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«تَسَحَّرُوا، فَإِنَّ فِي السَّحُورِ بَرَكَةً».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1923]
المزيــد ...
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin sahur".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1923]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan sahur shi ne cin (abin ci) a ƙarshen dare dan yin tanadi ga azimi; domin cewa a cikinsa akwai (albarka) alheri mai yawa na lada da sakamako, da tashi a ƙarshen dare dan addu'a, da ƙarfafuwa akan azimi, da nishaɗuwa gare shi, da kuma sauƙaƙa wahalarsa.