+ -

عَنْ زَيْدِ بْنِ ثَابِتٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ:
تَسَحَّرْنَا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، ثُمَّ قَامَ إِلَى الصَّلاةِ، قُلْتُ: كَمْ كَانَ بَيْنَ الأَذَانِ وَالسَّحُورِ؟ قَالَ: قَدْرُ خَمْسِينَ آيَةً.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1921]
المزيــد ...

Daga Zaidu ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Mun yi sahur tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan ya tashi zuwa sallah, na ce: Nawa ne tsakanin kiran sallah da sahur? ya ce: Gwargwadan ayoyi hamsin.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1921]

Bayani

Wasu daga sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun yi sahur tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tashi zuwa sallar Asuba. Sai Anas ya cewa Zaid ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi -: Nawane gwargwadan lokaci sahur tsakanin kiran sallah da iƙama? Sai Zaid ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Gwargwadan karanta ayoyi hamsin ne matsakaita, ba dogwaye ba ba kuma gajeru ba, ba karatu da gaggawa ba ba kuma a hankali ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar jinkirta sahur har zuwa gab da Asuba; domin idan ya jinkirta to anfanin jikin daga gare shi ya fi girma kuma anfaninsa a yinin ya fi yawa.
  2. Kwaɗayin sahabbai da haɗuwa da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan su yi koyi da shi.
  3. Kyakkyawar mu'amalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga sahabbansa, inda ya kasance yana cin (abin ci) tare da su.
  4. Lokacin kamewa shi ne ɓullowar alfijir.
  5. Faɗinsa: "Nawa ne tsakanin kiran sallah da sahur", abin nufi tsakanin sahur da iƙama; saboda faɗinsa a wani hadisn: "Nawa ne tsakanin gamawarsu daga sahur ɗinsu da kuma shigarsu sallah", hadisai sashinsu suna fassara sashi.
  6. AlMuhallab ya ce: A cikinsa akwai ƙaddara lokuta da ayyukan jiki, larabawa sun kasance suna ƙaddara lokuta da ayyuka kamar faɗinsu: Gwargwadan tatsar nonon akuya, da gwargwadan soke raƙumi, sai Zaid ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi - ya kauce daga hakan zuwa ƙaddarawa da karatu; dan nuni zuwa cewa wancan lokacin ya kasance lokacin ibada ne da karatu, da sun kasance suna ƙaddarawa da wanin aiki da ya ce misali: Gwargwadan daraja, ko ɗaya bisa uku ɗaya bisa biyar na awa.
  7. Ibnu Abi Jamrah ya ce: Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance yana duba abinda shi ne mafi sauƙi ga al'ummarsa sai ya aikata shi; domin cewa shi da bai yi sahur ba da sun bi shi sai ya yi wa wasunsu wahala, da kuma ya yi sahur a tsakiyar dare da ya yi wa wanda bacci yake rinjayarsa wahala zai iya kai shi zuwa barin sallar Asuba ko ya buƙatu zuwa ƙoƙarin rashin bacci.
Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الرومانية
Manufofin Fassarorin