عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه قَالَ:
كُنَّا نُخْرِجُ إِذْ كَانَ فِينَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ الْفِطْرِ، عَنْ كُلِّ صَغِيرٍ وَكَبِيرٍ، حُرٍّ أَوْ مَمْلُوكٍ، صَاعًا مِنْ طَعَامٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ أَقِطٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ زَبِيبٍ، فَلَمْ نَزَلْ نُخْرِجُهُ حَتَّى قَدِمَ عَلَيْنَا مُعَاوِيَةُ بْنُ أَبِي سُفْيَانَ رضي الله عنه حَاجًّا، أَوْ مُعْتَمِرًا فَكَلَّمَ النَّاسَ عَلَى الْمِنْبَرِ، فَكَانَ فِيمَا كَلَّمَ بِهِ النَّاسَ أَنْ قَالَ: إِنِّي أَرَى أَنَّ مُدَّيْنِ مِنْ سَمْرَاءِ الشَّامِ، تَعْدِلُ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، فَأَخَذَ النَّاسُ بِذَلِكَ، قَالَ أَبُو سَعِيدٍ: فَأَمَّا أَنَا فَلَا أَزَالُ أُخْرِجُهُ كَمَا كُنْتُ أُخْرِجُهُ، أَبَدًا مَا عِشْتُ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 985]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cikinmu, daga kowane ƙaramin (yaro) da babba, ɗa ne ko bawa, Sa’i na abinci, ko Sa’i na cukwi, ko Sa’i na sha'ir, ko Sa’i na dabino, ko Sa’i na zabibi, kuma bamu gushe ba muna fitar da shi har saida Mu'awiya ɗan Abu Sufyan - Allah Ya yarda da shi - ya gabato gurinmu yana mai aikin Hajji, ko yana mai Umarah sai ya yi wa mutane magana akan minbari, ya kasance daga abinda ya yi wa mutane magana da shi cewa ya ce: Lallai ni na ga cewa mudu biyu na alkamar Sham, sun yi daidai da sa'i ɗaya na dabino, sai mutane suka yi riko da hakan, Abu sa'id ya ce: Ammma ni ba zan gushe ba ina fitar da shi kamar yadda na kasance ina fitar da shi, muddin dai na rayu har abada.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 985]
Musulmai sun kasance suna fitar da zakkar fidda kai Sa’i ɗaya na abinci a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da zamanin Khalifofi masu shiryarwa a bayansa daga ƙaramin (yaro) da babba. Abin cin su ya kasance sha'ir ne da (zabibi): Bushasshen inibi, da (cukwi): Busasshen nono da kuma dabino. Gwargwadan Sa’i mudu huɗu ne, mudu kuma ya yi daidai da cikin tafi biyu na namiji madaidaici (ba babba ba ba kuma ƙarami ba). Lokacin da Mu'awiya - Allah Ya yarda da shi - ya zo Madina alhali shi yana Khalifa, kuma alkamar Sham ta yi yawa, sai ya yi huɗuba sai ya ce: Lallai ni ina ganin cewa mudu biyu na alkamar Sham (rabin Sa’i), sun yi daidai da Sa’i ɗaya na dabino, sai mutane suka yi riƙo da hakan. Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Amma ni ba zan gushe ba ina fitar da shi kamar yadda na kasance ina fitar da shi a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi har abada muddin dai ina raye.