+ -

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ:
فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ الفِطْرِ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ، عَلَى العَبْدِ وَالحُرِّ، وَالذَّكَرِ وَالأُنْثَى، وَالصَّغِيرِ وَالكَبِيرِ مِنَ المُسْلِمِينَ، وَأَمَرَ بِهَا أَنْ تُؤَدَّى قَبْلَ خُرُوجِ النَّاسِ إِلَى الصَّلاَةِ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1503]
المزيــد ...

Daga Ɗan Umar - Allah ya yarda da su - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino, ko Sa'i na alkama, akan bawa da ɗa, namiji da mace, ƙarami da babba cikin musulmai, kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallah.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1503]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai bayan (azimin) Ramadan, ita gwargwadan Sa'i ne (wanda) awonsa yakai mudun Nabiyyi huɗu. Mudun Nabiyyi: (Shi ne) cikin tafukan mutum madaidaici, na dabino ko alkama akan kowane musulmi; ɗa da bawa, namiji da mace, ƙarami da babba, hakan ga wanda a wajensa akwai abinda ya rage daga abin cin yininsa da darensa, (zai fitarwa) kansa da kuma wanda yake kula da su. Kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallar idi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili Asami الغوجاراتية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Zakkar fidda kai ta azimi tana wajaba a fitar wa yaro ita da babba, da ɗa da bawa, kuma ana yi wa waliyyin (yaro) da mamallakin (bawa) umarni da ita, kuma mutum yana fitarwa kansa da 'ya'yansa da wanda ciyarwarsu take wajaba akansa.
  2. Zakkar fidda kai ba ta wajaba daga ɗan tayi, saidai an so (a fitar masa).
  3. Bayanin abinda ake fitarwa a zakkar fidda kai, shi ne abincin mutane na al'ada.
  4. Wajabcin fidda ita kafin sallar idi, abinda ya fi ta kasance a safiyar idi, kuma fitar da ita yana halatta kafin idi da kwana ɗaya ko kwanaki biyu.