عن أبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَا يَحِلُّ لِامْرَأَةٍ مُسْلِمَةٍ تُسَافِرُ مَسِيرَةَ لَيْلَةٍ إِلَّا وَمَعَهَا رَجُلٌ ذُو حُرْمَةٍ مِنْهَا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1339]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ba ya halatta ga wata mace musulma ta yi tafiyar dare (ɗaya) sai a tare da ita akwai namiji muharraminta".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1339]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa yana haramta akan mace musilma ta yi tafiyar dare (daya) sai idan akwai namji muharraminta tare da ita.