+ -

عن عائشة وأم سلمة رضي الله عنهما «أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان يُدْرِكُهُ الفجر وهو جُنٌبٌ من أهله، ثم يغتسل ويصوم ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Nana Aisha da Ummu Salam Allah ya yarda da su Daga Annabi : " Asuba tana Riske shi a halin yana cikin Janaba daga Ahalinsa, Sannan yayi Wanka yayi Sallah kuma ya yi Azumi"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Nana aisha da Ummu Salama Suna Bamu labari cewa Annabi ya kasance yana tarawa da iyalinsa cikin dare, wani lokaci ma Asuba tana riskassa a halin yana cikin Janaba baiyi wanka ba kuma ya cika Azuminsa kuma baya ramawa, kuma ya kasance ya basu Labari ne sabida bawa Marwan Dan Hakam Amsa lokacin da ya aiko musu da tambayar; don ya tambayesu hakan. kuma wannan Hukunci cikin watan Azumi ne da waninsa ma.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin