عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما قال: «نهى رسول الله صلى الله عليه وسلم عن الْوِصَالِ، قالوا: إنك تواصل؟ قال: إني لَسْتُ كَهَيْئَتِكُمْ، إني أُطْعَمُ وَأُسْقَى». وفي رواية أبي سعيد الخدري رضي الله عنه : «فَأَيُّكُمْ أراد أن يواصل فليواصل إلى السَّحَرِ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Umar - Allah ya yarda da shi - zuwa ga Annabi : "nnabi _ Tsira da Amincin Allah ya yarda da shi - Ya hana Sabi Zarce a Azumi sai suka ce : Cewa ai kaima kana yi sai ya ce: cewa ni ai ba irinku bane , ni ai ana ciyar da ni kuma ana shayar da ni"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya hana Sahabban sa sabi zarce a cikin Azumi don jin kai a gare su da kuma tausaya musu sai dai Sahabbai saboda sonsu da aikin Alkairi da duk abinda zai kusanta su zuwa ga Allah shi yasa suke kwadayi sabi zarce dincikin Azumi don koyi da Annabi kasancewar sa yana yi don haka suka ce: Ai kaima kanayi sai ya basu labari da cewa yana da wanda yake ciyar da shi kuma ya ke Shayar da shi da abinda zai maye gurbin abinci da shi, to duk wanda yake son yayi to yayi zuwa lokacin Suhur to ita Shari'ar Musulunci Mai sauki ce Mai sauki ce babu wahala a cikinta, kuma ba bu shige da kutsa kai cikin abunda bai sani ba domin cikin wannan akwai Azabtar da kai da bawa kai wahala, kuma Allah bai dorawa rai ba sai abunda zata iya yi, kuma saukakawa da rangwantawa yafi sa aiki ya dawwama kuma yafi sanya aiki kubuta daga gajiyawa da kosawa kuma cikin hakan akwai Adalci wanda shi Allah yasanya a bayan Kasa, kuma shi ne abawa Allah hakkinsa da ya nema na Ibada, da kuma bawa rai bukatar ta na kashin kanta.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin