lis din Hadisai

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance damantawa tana kayatar da shi, a sanya takalminsa, da taje kansa, da tsarkinsa, kai da sha'aninsa duka.
عربي Turanci urdu
Na kiyaye raka'o'i goma daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -*: Raka'a biyu kafin Azahar, da raka'a biyu a bayan azahar, da raka'a biyu bayan Magariba a gidansa, da raka'a biyu bayan Issha' a gidansa, da raka'a biyu kafin sallar Asuba, wani lokaci ne ba'a shiga wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa, Nana Hafsat ta zantar da ni cewa idan ladani ya yi kiran sallah, alfijir ya bullo zai yi sallah raka'a biyu, a wani lafazin: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana sallah bayan Juma'a raka'a biyu.
عربي Turanci urdu
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya tashi da daddare yana goge bakinsa da asuwaki.
عربي Turanci urdu
"Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, azaba ta tabbata ga larabawa daga sharrin da ya kusanto, a yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju kwatankwacin hakan"* sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda yake biye da shi. Zainab 'yar Jahsh ta ce : Sai na ce ya Manzon Allah: Shin zamu halaka alhali a cikinmu akwai salihai? ya ce: "Eh, idan barna ta yi yawa".
عربي Turanci urdu
Lallai" Annabi -tsira da aminci- ya kasance a wata tafiya, sai ya ya yi sallar Issha'i, ya karanta Wattini a daya daga cikin raka'oi biyun sallar, ban taba jin wani mai adadin sauti, ko dadin karatu kamar shi ba"
عربي Turanci urdu
Cewa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan yana sallah yana buɗa tsakanin hannayensa har sai farin hammatarsa ya bayyana.
عربي Turanci urdu
Na kasance ina wanka ni da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga kwarya (abin wanka) daya mu duka biyun muna da janaba, ya kasance yana umartata, sai insa gwafso, sai ya rungumeni alhali ni ina al’ada, *ya kasance yana fito min da kansa alhali shi yana i'itikafi sai in wanke masa shi alhali ina al’ada.
عربي Turanci urdu
Cewa Annabi –SAW- ya kasance yana bacci a farkon dare, yana tashi a qarshen dare yana sallah
عربي Turanci urdu
Idan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya rasa salla daga jin zafi ko wani abu da daddare, zai yi raka’a goma sha biyu da rana.
عربي Turanci urdu
Daga Abdullah bn Abbas - Allah ya yarda da shi - ya ce: "Annabi - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi salla a kan kabari bayan an binne shi, don haka yana da shekara hudu a kanta."
عربي Turanci urdu
Annabi ya kasance yana Karantawa a Sallar Asubar Ranar Jumua : Suratu Sajada, kuma Suratul Insan
عربي Turanci urdu
Hannun dama na Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance don tsarkake shi da abincinsa, kuma hannun hagu na wofintar da abin da yake cutarwa
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana shiga bayan gida, sai ni da wani yaro sa'ana mu ɗaukar masa salka ta ruwa da kuma sanda sai ya yi tsarki da ruwa.
عربي Turanci urdu
Ya nuna min a cikin mafarki cewa kun sanya shara, sai maza biyu suka zo wurina, ɗayansu ya fi ɗayan girma, don haka na kusanci su biyun
عربي Turanci urdu
Annabi _ Tsira da Amincin Allah ya yarda da shi - Ya hana Sabi Zarce a Azumi sai suka ce : Cewa ai kaima kana yi sai ya ce: cewa ni ai ba irinku bane , ni ai ana ciyar da ni kuma ana shayar da ni
عربي Turanci urdu
"Na kasance ina Sallah tare da Annabi -Amincin Allah a gare shi- Salloli Sallarsa ta kasance tsakatsaki ce haka Hudubarsa tsakatsaki ce"
عربي Turanci urdu
Na yi salla tare da Annabi -SAW- a wani dare, kuma ya tsawaita tsayuwa har sai na damu da wani abu mara kyau! Aka ce: Me kuke sha'awa? Ya ce: Na so in zauna in barshi.Daga Ibn Masoud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Na yi salla tare da Annabi -SAW- a wani dare, kuma ya tsawaita tsayuwa har sai na damu da wani abu mara kyau! Aka ce: Me kuke sha'awa? Ya ce: Na so in zauna in barshi.
عربي Turanci urdu
Cewa wasu mutane daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun tambayi matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da aikinsa a ɓoye? sai sashinsu ya ce: Ba zan auri mata ba, sashinsu kuma ya ce: Ba zan ci nama ba, sashinsu ya ce: Ba zan yi bacci akan shinfiɗa ba, sai ya godewa Allah kuma ya yi yabo gare shi, sai ya ce: @"Me ya samu wasu mutane ne sun ce kaza da kaza? sai dai cewa ni ina sallah kuma ina bacci, ina azimi ina buɗe baki, kuma ina auren mata, wanda ya ƙi sunnata to ba ya tare da ni".
عربي Turanci urdu