عَنْ زَيْنَبَ بِنْتِ جَحْشٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْها أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ دَخَلَ عَلَيْهَا فَزِعًا يَقُولُ:
«لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَيْلٌ لِلْعَرَبِ مِنْ شَرٍّ قَدِ اقْتَرَبَ، فُتِحَ اليَوْمَ مِنْ رَدْمِ يَأْجُوجَ وَمَأْجُوجَ مِثْلُ هَذِهِ» وَحَلَّقَ بِإِصْبَعِهِ الإِبْهَامِ وَالَّتِي تَلِيهَا، قَالَتْ زَيْنَبُ بِنْتُ جَحْشٍ فَقُلْتُ يَا رَسُولَ اللَّهِ: أَنَهْلِكُ وَفِينَا الصَّالِحُونَ؟ قَالَ: «نَعَمْ إِذَا كَثُرَ الخَبَثُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3346]
المزيــد ...
Daga Zainab 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga gurinta a firgice yana cewa;
"Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, azaba ta tabbata ga larabawa daga sharrin da ya kusanto, a yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju kwatankwacin hakan" sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda yake biye da shi.
Zainab 'yar Jahsh ta ce : Sai na ce ya Manzon Allah: Shin zamu halaka alhali a cikinmu akwai salihai? ya ce: "Eh, idan barna ta yi yawa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3346]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga gurin Zainab 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - a firgice a tsorace, alhali shi yana cewa: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan sanarwa da tinanin afkuwar wani al'amari abin ki da zai faru, kuma babu tsira daga gare shi sai fakewa ga Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Kaico ya tabbata ga Larabawa daga wani sharrin da afkuwarsa ya kusanto, yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju, shi ne katangar da Zulkarnaini ya ginata, misalin wannan; sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda ke biye da shi. Sai Zainab - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Yaya Allah Zai halakar da mu alhali a cikinmu akwai muminai na gari? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mata: Idan barna ta yi yawa da fasikanci da fajirci da sabo, da zina, da giya, da wasunsu, to halaka zata game kowa da kowa.