عن أبِي هريرة رضي اللَّه عنه: سمعتُ النبِيّ صلى الله عليه وسلم يقول:
«الفِطْرَةُ خمسٌ: الخِتَانُ والاستحدادُ وقصُّ الشَّارِبِ وتقليمُ الأظفارِ وَنَتْفُ الآبَاطِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5891]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Dabi'a (ta addinin Musulunci ) guda biyar ce: Kaciya da aske gashin mara, da rage gashin baki, da yanke farata, da tsige gashin hammata".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5891]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana ɗabi'u biyar daga addinin Musulunci da kuma sunnonin manzanni:
Na farkonsu: Kaciya, ita ce yanke fatar da ta ƙaru a kan azzakari wajen kan kaciya, da kuma yanke kan fata a farjin mace a saman bigiren mashigar azzakari.
Na biyunsu: Aske gashin mara, shi ne aske gashin mara wanda ke gefen gaba.
Na ukunsu: Rage gashin baki, shi ne rage abin da ya tsiro a kan leɓen sama na namiji inda leɓe yake bayyana.
Na huɗunsu: Yanke farata.
Na biyar ɗinsu: Aske gashin hammata.