+ -

عن عائشة رضي الله عنها قالت: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«السِّوَاكُ مَطْهَرَةٌ لِلْفَمِ، مَرْضَاةٌ لِلرَّبِّ».

[صحيح] - [رواه النسائي وأحمد] - [مسند أحمد: 24203]
المزيــد ...

Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yace:
"Asiwaki mai tsarkake baki ne, mai sa yardar Ubangiji ne".

Ingantacce ne - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sanar damu cewa tsaftace hakora da itaciyar urak da makamancinta yana tsaftace baki daga datti da wari wadanda suke abin ki. Kuma cewa shi yana daga sabubban yardar Allah ga bawa; domin cewa a cikinsa akwai biyayya ga Allah da amsa umarninSa, da kuma abinda ke cikinsa na tsaftar da Allah - Madaukakin sarki - yake son ta.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية القيرقيزية النيبالية اليوروبا الليتوانية الدرية الصومالية الطاجيكية الكينياروندا الرومانية المجرية التشيكية المالاجاشية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar asiwaki, da kwadaitarwar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi ga al'ummarsa da yawaitawa hakan.
  2. Abinda yafi ga asiwaki shi ne yin amfani da itacan urak (kirya), yin amfani da makilin da burush yana tsayawa a madadinta.