عَنْ عِمْرَانَ بْنِ حُصَيْنٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ:
جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: السَّلَامُ عَلَيْكُمْ، فَرَدَّ عَلَيْهِ ثُمَّ جَلَسَ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «عَشْرٌ» ثُمَّ جَاءَ آخَرُ فَقَالَ: السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ، فَرَدَّ عَلَيْهِ فَجَلَسَ، فَقَالَ: «عِشْرُونَ» ثُمَّ جَاءَ آخَرُ فَقَالَ: السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ وَبَرَكَاتُهُ، فَرَدَّ عَلَيْهِ فَجَلَسَ، فَقَالَ: «ثَلَاثُونَ».
[حسن] - [رواه أبو داود والترمذي وأحمد والدارمي] - [سنن أبي داود: 5195]
المزيــد ...
Daga Imran ɗan Husain - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Assalamu alaikum (Aminci ya tabbata agare ku), sai ya amsa masa sannan ya zauna, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Goma» Sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai ya ce: «Ashirin», sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai ya ce: «Talatin».
[Hasan ne] - - [سنن أبي داود - 5195]
Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Assalamu alaikum, (Aminci ya tabbata agare ku) sai ya amsa masa sannan ya zauna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: An rubuta masa lada goma, sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah, (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Yana da lada ashirin, sannan wani ya zo sai ya ce: (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Yana da lada talatin; wato kowane lafazi yana da lada goma.