عَنْ أَبِي قَتَادَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«الرُّؤْيَا الصَّالِحَةُ مِنَ اللَّهِ، وَالحُلُمُ مِنَ الشَّيْطَانِ، فَإِذَا حَلَمَ أَحَدُكُمْ حُلُمًا يَخَافُهُ فَلْيَبْصُقْ عَنْ يَسَارِهِ، وَلْيَتَعَوَّذْ بِاللَّهِ مِنْ شَرِّهَا، فَإِنَّهَا لاَ تَضُرُّهُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3292]
المزيــد ...
Daga Abu Katadah- Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mafarki na gari daga Allah ne, mummunan mafarki kuwa daga Shaiɗan ne, idan ɗayanku ya yi mummunan mafarkin da yake jin tsoronsa to ya yi tofi a hagunsa, kuma ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, to cewa shi ba zai cutar da shi ba".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3292]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa kyakkyawan mafarki mai faranta rai a cikin mafarki to daga Allah ne, mummunan mafarki shi ne mafarkin da yake ƙi kuma yake baƙanta rai to daga Shaiɗan ne.
Wanda ya ga abinda yake ƙinsa (a mafarki) to ya yi tofi a ɓangaren hagunsa, kuma ya nemi tsarin Allah daga sharrinsu; to cewa shi ba zai cutar da shi ba, inda Allah Ya sanya abinda aka ambata (na Addu’a) sababi ne na kuɓuta daga abin ƙi na abinda jeranta akan mafarki.