عن ابن عمر رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«أحْفُوا الشَّوَارِبَ وأَعْفُوا اللِّحَى».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 259]
المزيــد ...
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ku rage gashin baki, ku cika gemu".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 259]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana umarni da rage gashin baki, kuma kada a barshi, kawai a rageshi, kuma a kai matuƙa a hakan.
A ɗaya ɓangaren kuma yana umarni da cika gemu da kuma barinsa a cike.