عَنْ حُذَيْفَةَ رضي الله عنه قَالَ:
كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا قَامَ مِنَ اللَّيْلِ يَشُوصُ فَاهُ بِالسِّوَاكِ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 245]
المزيــد ...
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya tashi da daddare yana goge bakinsa da asuwaki.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 245]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance lokuta da yawa yana yin asuwaki kuma yana umarni da a yi shi, hakan yana karfafuwa a wasu lokuta, daga cikinsu: Asuwaki lokacin tashi da daddare, lokacin da tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cuccuɗawa kuma yana wanke bakinsa da asuwaki.