عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ:
حَفِظْتُ مِنَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَشْرَ رَكَعَاتٍ: رَكْعَتَيْنِ قَبْلَ الظُّهْرِ، وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَهَا، وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَ المَغْرِبِ فِي بَيْتِهِ، وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَ العِشَاءِ فِي بَيْتِهِ، وَرَكْعَتَيْنِ قَبْلَ صَلاَةِ الصُّبْحِ، وَكَانَتْ سَاعَةً لاَ يُدْخَلُ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِيهَا، حَدَّثَتْنِي حَفْصَةُ أَنَّهُ كَانَ إِذَا أَذَّنَ المُؤَذِّنُ وَطَلَعَ الفَجْرُ صَلَّى رَكْعَتَيْنِ، وَفِي لَفْظٍ: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يُصَلِّي بَعْدَ الْجُمُعَةِ رَكْعَتَيْنِ.
[صحيح] - [متفق عليه بجميع رواياته] - [صحيح البخاري: 1180]
المزيــد ...
Daga Dan Umar - Allah ya yarda da su - ya ce:
Na kiyaye raka'o'i goma daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Raka'a biyu kafin Azahar, da raka'a biyu a bayan azahar, da raka'a biyu bayan Magariba a gidansa, da raka'a biyu bayan Issha' a gidansa, da raka'a biyu kafin sallar Asuba, wani lokaci ne ba'a shiga wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa, Nana Hafsat ta zantar da ni cewa idan ladani ya yi kiran sallah, alfijir ya bullo zai yi sallah raka'a biyu, a wani lafazin: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana sallah bayan Juma'a raka'a biyu.
[Ingantacce ne] - [Buhari da Muslim ne suka rawaito shi da dukkan ruwayoyin sa] - [صحيح البخاري - 1180]
Abdullahi Dan Umar - Allah Ya yarda da su - yana bayyana: Cewa daga nafilfilin da ya haddacesu daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - raka'o'i goma ana ambatansu sunnoni ratibai, raka'a biyu kafin Azahar, da raka'a biyu a bayan azahar, da raka'a biyu bayan Magariba a gidansa, da raka'a biyu bayan Isha'i a gidansa, da raka'a biyu kafin Asuba, raka'o'i goma sun cika kenan. Amma sallar Juma'a yana yin sallah raka'a biyu a bayanta.