kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

Na kiyaye raka'o'i goma daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -*: Raka'a biyu kafin Azahar, da raka'a biyu a bayan azahar, da raka'a biyu bayan Magariba a gidansa, da raka'a biyu bayan Issha' a gidansa, da raka'a biyu kafin sallar Asuba, wani lokaci ne ba'a shiga wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa, Nana Hafsat ta zantar da ni cewa idan ladani ya yi kiran sallah, alfijir ya bullo zai yi sallah raka'a biyu, a wani lafazin: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana sallah bayan Juma'a raka'a biyu.
عربي Turanci urdu
Lallai" Annabi -tsira da aminci- ya kasance a wata tafiya, sai ya ya yi sallar Issha'i, ya karanta Wattini a daya daga cikin raka'oi biyun sallar, ban taba jin wani mai adadin sauti, ko dadin karatu kamar shi ba"
عربي Turanci urdu
Cewa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan yana sallah yana buɗa tsakanin hannayensa har sai farin hammatarsa ya bayyana.
عربي Turanci urdu
Cewa Annabi –SAW- ya kasance yana bacci a farkon dare, yana tashi a qarshen dare yana sallah
عربي Turanci urdu
Idan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya rasa salla daga jin zafi ko wani abu da daddare, zai yi raka’a goma sha biyu da rana.
عربي Turanci urdu
Annabi ya kasance yana Karantawa a Sallar Asubar Ranar Jumua : Suratu Sajada, kuma Suratul Insan
عربي Turanci urdu
"Na kasance ina Sallah tare da Annabi -Amincin Allah a gare shi- Salloli Sallarsa ta kasance tsakatsaki ce haka Hudubarsa tsakatsaki ce"
عربي Turanci urdu
Na yi salla tare da Annabi -SAW- a wani dare, kuma ya tsawaita tsayuwa har sai na damu da wani abu mara kyau! Aka ce: Me kuke sha'awa? Ya ce: Na so in zauna in barshi.Daga Ibn Masoud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Na yi salla tare da Annabi -SAW- a wani dare, kuma ya tsawaita tsayuwa har sai na damu da wani abu mara kyau! Aka ce: Me kuke sha'awa? Ya ce: Na so in zauna in barshi.
عربي Turanci urdu