+ -

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مَالِكٍ ابْنِ بُحَيْنَةَ رضي الله عنه:
أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ إِذَا صَلَّى فَرَّجَ بَيْنَ يَدَيْهِ حَتَّى يَبْدُوَ بَيَاضُ إِبْطَيْهِ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 390]
المزيــد ...

Daga Abdullahi ɗan Malik ɗan Buhainah - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan yana sallah yana buɗa tsakanin hannayensa har sai farin hammatarsa ya bayyana.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 390]

Bayani

Tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya kasance idan zai yi sujjada yana buɗa tsakanin hannayensa a tsakiyar sujjada; sai kowanne hannu ya nisanta daga gefan da yake biye masa, kwatankwacin fukafukai biyu, har launin fatar hammatarsa ya bayyana; wannan yana daga kai matuƙa a nisantar da zira'i biyu da kuma nisantar da su daga sasanninsu.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الدرية الصومالية Kinyarwanda الرومانية Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so wannan yanayin a cikin sujjada, shi ne nisantar da damatsansa biyu daga sasanninsa.
  2. Mamun da na kusa da shi yake cutuwa da nisantarwar to ba'a shar’anta masa hakan ba.
  3. Akwai hikimomi da fa'idoji masu yawa a cikin nisantar a cikin sujjada, daga cikinsu:
  4. Bayyanar da nishaɗi da kwaɗayi a cikin sallah, kuma idan ya dogara akan dukkan gaɓɓan sujjada sai kowacce gaɓa ta ɗauki haƙƙinta daga bauta. Akace: Hikima a cikin hakan ya yi kama da tawali'u, kuma mafi isuwa a cikin tabbatar da goshi da hanci a ƙasa, kuma dan banbance kowacce gaɓa da kanta.